An gano kwarangwal ɗin wani attajiri da bawansa da suka halaka shekara 2000

A Pompeii ne hukumomi suka bada sanarwar gano kwarangwal ɗin wani attajiri da bawansa da aka yi hasashen suna ƙoƙarin tsira ne daga aman wuta na dutsen Vesuvius, kusan shekaru 2000 da suka gabata.

An haƙo su ne a wani fili na masu ilimin kimiyar kayan tarihi da yake ƙasar Italy, a ranar Asabar.

Jaridar Associate Press ta ruwaito cewa an gano ƙasusuwan kai da sauran sassan mutanen guda biyu, a haƙe-hake da ake na gurin da ake zaton wani tsohon gidan alfarma ne, da yake kallon tekun Mediterranean dake wajen birnin Roma, wanda amon wutar dutse ta lalata garin a shekara 79 bayan bacewar Annabi Isa AS.

A dai wannan guri ne a shekara 2017 aka haƙo wasu kwarangwal na wasu dawaki guda uku.

Tags:
%d bloggers like this: