Hanyar Abuja Zuwa Kano Ba Za Ta Kammalu Ba A Zamanin Buhari

  • Home
  • Labarai
  • Hanyar Abuja Zuwa Kano Ba Za Ta Kammalu Ba A Zamanin Buhari

Duk tsawon lokacin da aka dauka ana aikin gyaran titin Abuja zuwa Kano, gwamnati ta tabbatar ba za ta kammalu ba a zamanin shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ba.

Hakan ya fito daga bakin ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kaduna, yayin da wani babban ayarin gwamnatin tarayya ya ziyarci inda ake ayyukan

.

“Nan da shekarar 2022 ne za a kammala hanyar da ke tsakanin Kaduna da Zaria, wanda wannan babban ci gaba ne.

“A 2023 za a kammala hanayar da ta tashi daga Kaduna ta dangane ga Kano, sai kuma a 2025 za a kammala hanyar Abuja zuwa Kano baki ɗayanta,” in ji Fashola.

Wannan babbar tawagar gwamnatin tarayyar da aka sanar da za su ziyarci guraren da ake aikin gyaran titin Kaduna zuwa Kano sun nuna gamsu da yadda ake gudanar da aikin, duk kuwa da cewa dinbin al’umma na kokawa na yadda aikin ke tafiyar hawainiya, baya ga asarar rayuka da titin yake janyowa.

Shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari, wanda ke cikin tawagar ya ce “Mun gamsu da ingancin aikin a wuraren da aka kammala, duk da cewa akwai ‘yan matsaloli.”

Ba a san wane irin kokari gwamnatin tarayyar za ta yi ba na warware matsalolin da shugaban ma’aikatan ya amince akwai su ba. Wannan hanya na daga cikin hanyoyi da mutane ke zirga-zirga a kanta a Arewa fiye da wani titi, wanda kamata ya yi gwamnati ta bata mihimmancin da ya kamata.

%d bloggers like this: