GWAJIN RIGAKAFIN KORONA YA YI NASARA

Bayan nan da suke fitowa na baya-bayan na nuna cewa rigakafin cutar konona da kamfanin Pfizer da BioNTech suka sama ya nuna tasirin maganin wajen maganin cutar ba tare da wata illa ba.

Kafar BBC Hausa ta ruwaito cewa masu kula da lafiya a duniya za su iya fara kokarin amincewa da maganin domin amfani da shi a yaki da ake da cutar ta korona.

Gwajin ya nuna tasirin maganin kan mutane daban-daban ba tare da wata babbar illa ba, wanda haka babbar nasara ce wajen kawar da wannan cuta.

An yi gwajin rigakafin a kan mutane sama da 43, 000 a kasashe shida.

Rahoton BBC ya nuna kamfanonin Pfizer da BioNTech na fatan samar da kusan alluran rigakafin sama da miliyan 50 a cikin wannan shekara, sannan su samar da fiye da biliyan daya a shekara 2021.

%d bloggers like this: