Dogon Yajin Aiki Ya Sa Dalibai Amayar Da Bacin Ransu A Twitter

  • Home
  • Labarai
  • Dogon Yajin Aiki Ya Sa Dalibai Amayar Da Bacin Ransu A Twitter

A yayin da yajin aikin Malam jami’oi ke shiga wata na takwas, dalibai sun fara kokawa na zaman gidan da suke. A yau Laraba treads na Twitter da yake haskawa shi ne FG and ASUU, wanda matasa ke ta musayar yawu kan batun yajin aikin.

Wasu na ganin laifin gwamnatin tarayya, a inda wasu na kalubalantar ASUU kan ba su da godiyar Allah. Ga abin da wasu daga cikin masu mahawarar ke cewa.

Mohammed Jammal na ganin hauka ne a ce har yanzu ƙungiyar ASUU na yajin aiki, a cewarsa, duk da ya ɗora laifi a kan gwamnatin ƙasar, ya kuma ɗora laifin yajin aikin a kan ƙungiyar ta ASUU.

Wani shafin ASUU da ake zaton na bogi ne ya zunguro sama da kara inda a shafin ake bawa dalibai shawara da su nemi abin yi. To amma kungiyar ASUU ta fito ta karyata cewa ba ita ke da wanda Tuwita ba.

Ko yaya abin yake, dalibai sun kosa da zaman kashe wando da suke. Akwai bukatar bangarorin biyu su yi duba kan masalahar daliban.

%d bloggers like this: