Za a magance matsalar tsaron Najeriya-Muhammadu Buhari

  • Home
  • Labarai
  • Za a magance matsalar tsaron Najeriya-Muhammadu Buhari

Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ba wa ‘yan ƙasa tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi abin da ya dace dangane matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Shugaban ƙasar ya yi magana ne yayin taron majalisar koli a kan harkokin tsaro da ya jagoranta a ranar Talata.

Hakazalika ya yi jawabi dangane da rikicin EndSARS da aka sha fama a watan da ya gabata. Shugaban ƙasar ya ce gwamnati za ta ɗauki matakan gyara al’amurra don ganin ba a ƙara samun wata matsala ba da za ta iya tayar da tarzoma.

%d bloggers like this: