Youtube: Daji Ba A Maka Kyaure

Durƙushewar kasuwar finafinan bidiyo ta sa masu shirya finafinai a duniya su ka bazama neman mafita. Yawanci sai su ka rungumi  harkar sakin bidiyo a intanet, su na karɓar kamasho cikin tsarin ‘Video On Demand’ ko ‘PPV’ ko ‘Live Stream’ da sauran su.

Wannan ta sa aka samu hamshaƙan dandalai irin su Netflix da Amazon Prime da Hulu da su Vimeo da kuma YouTube su na ta samun tagomashi a wannan lokaci.  

Duniyar finafinan Hausa ma ba a bar ta a baya ba. Da dama masu shirya finafinan masana’antar ta Kannywood sun shiga cikin sha’anin sakin finafinan su a dandalin YouTube domin kowa ya gani.

Wataƙila sun zaɓi YouTube ne saboda ya fi araha ko kuma ya fi shahara, sai su ka tafi gare shi yanzu su na cin duniyar su da tsinke.  YouTube wani dandalin intanet ne da ke bada dama ga kowa ya aza bidiyo ko ya kalla ta kwamfuta ko ta waya ko a na’urar nan ta musamman da ake kira SmartTv.   

Dandalin YouTube shi ne na biyu a duniya bisa ma’aunin Alexa, domin ya na samun maziyarta aƙalla biliyan 2 duk wata. Ka na iya saka bidiyo ya zamana ana iya kallon sa a duk faɗin duniya nan take.  

An buɗe dandalin a shekarar 2005, sannan a cikin 2006, kamfanin Google ya saye shi a kan kuɗi dala biliyan 1.65.  Wataƙila saboda ganin yadda masu shirya fim ɗin Hausa su ka raja’a ga dandalin YouTube ɗin ne ya sa Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta wasa takobin tantance finafinai da kuma masu shirya finafinan da ake yaɗawa a dandalin.

Hukumar ta ƙara da cewar tuni ta tanadi hanyoyin da za ta riƙa bibiyar irin waɗannan finfinai.  Wannan dai  ba ƙaramin aiki ba ne. Ba wai ina cewa hukumar ba za  ta iya aiwatar da hakan ba ne, sai dai hakan tamkar ƙara wa Barno dawaki ne, domin kuwa shi YouTube ya fi ƙara ƙarfi idan akwai masu bibiyar sa ta kowace fuska, walau saka ido ko kallo ko ɗora bidiyo.

Ta hakan ne ko da su masu bidiyoyin ba su samu komai daga sa idon da aka yi masu ba, kamfanin zai amfana ƙwarai.  An bayyana cewar a cikin 2019 kamfanin YouTube ya samu ribar dala biliyan 15 mafi yawa daga albarkacin masu kai ziyara dandalin ya samu. Kuma an yi ƙididdigar cewa duk minti ɗaya, ana hawar da bidiyoyin da su ka kai kimanin tsawon minti 500. Kenan a tsawon awa ɗaya ana iya hawar da bidiyo na tsawon awanni 30,000. Daga ciki waɗannan, mintuna nawa ne hukumar ke da ƙarfin ikon bibiya?  

Ba za mu ce kai tsaye tsarin zai yiwu ko ba zai yiwu ba,  sai dai tabbaci ne gatarin senso zai dira ne kurum ga wasu ƙalilan da ake ganin su ne fitattu a harkar waɗanda ake ganin kamar tashar su ta samu karɓuwa.  

Linzami ya fi ƙarfin bakin kaza. Rigimar da hukumar ke son ɗaukowa dangane da YouTube ya shallake hurumin ta. Ko da kuwa hurumin nata ya ba ta ikon yin haka, to ƙarshen ta haihuwar guzuma abin zai haifar.  Haka kuma,  ko da hukumar ta yi nasarar aiwatar da tsarin sa ido ko daƙile masu shirya fim ɗin Hausa a  YouTube, to akwai wasu kafafen intanet sama da dubu biyu da su ke aiki kwabo da kwabo irin YouTube ɗin.  

Ya kamata senso ta fahimci babban dalilin da ya sa masu fim ɗin Hausa a yanzu su ka raja’a zuwa ga YouTube sannan ta magance musu matsalar. Za mu iya cewa dalilin da ya sa su ke bozo a YouTube bai wuce  kwaɗayin samun ɗan abin da ake samu daga tallace-tallacen da ake watsa wa masu kallo ba.

Wannan kuwa bai wuce ladan gaɓe daga maƙudan kuɗin da YouTube ɗin ke samu ba.  Ladan gaɓen nan ma fa ba haka ziƙau ake bayar da shi ba, sai tasha ta cike wasu sharuɗɗa da su ka haɗa da tara mabiya aƙalla dubu tare da samun bidiyon sa an kalle shi na aƙalla awanni 4,000 a cikin shekara guda.

Kafin mutum ya cika wannan sharaɗi kuwa, sai ya yi jan aiki tare da kai gwauro da mari tsakanin gangan da gangariyanci.  Da a ce za su samu tallafin hukumar ana karɓar finafinan su ko da a tashar talabijin ta ARTV ne, da na tabbata ba za su riƙa haƙilon sanyawa a karan kaɗa miyar YouTube ba.  

Ta wata fuskar kuma, idan gwamnati ta ga dama, ta na iya aza takunkumi ga duk kafar intanet da ta ke ganin za ta zame mata barazana wajen tafiyar da sha’anin mulkin ta. Shi kan sa YouTube ya na cikin waɗanda aka sha garƙama wa takunkumi a ƙasashe kamar su Chana, Denmak, Pakistan, Iran da sauran su. Sai dai duk da ɗimbin kuɗin da ake halakarwa wajen tabbatar da wannan ƙudiri, ana samun masu kunnen ƙashi da ke yin ɗanwaken zagaye, su na shiga dandalin ta bayan fage, watau ‘tunnel’.  

Idan da senso za ta ɗauki shawara, da sai na ce maimakon ƙoƙarin yi wa daji ƙyaure, ya dace ta fito da wasu tsare-tsare da za su farfaɗo da martabar sana’ar fim tare da ƙara inganta tsabtace ta, ta yadda ko da a duniyar wata mutum zai shirya fim ɗin sa, zai yi la’akari da addini da al’adun mutanen Hausawa.

Idan ba haka ba, yaya hukumar za ta yi idan masu shirya finafinan su ka yi gudun hijira zuwa wasu wuraren da ba ta da hurumi su ka shirya fim ɗin su sannan su ka ɗora a YouTube ɗin, mutanen Kano su na shiga su na kalla?  Ta yaya za ta iya hana aukuwar haka? Ta yiwu dai, kamar yadda na ambata a sama, waɗanda kurar su ta yi kuka ne kaɗai za su ji a jikin su.  

A ƙarshe, ina kira ga hukumar senso, ya kamata ta ƙara zama gata ga masu shirya fim a YouTube ta yadda za su daina faɗi-tashi su samu cin moriyar abin da su ke yi. Domin a yanzu dai, masu samun tagomashi a cikin abin ba su taka kara sun karya ba.  

Hukuma na iya matsa wa YouTube su ƙara wa masu finafinan Hausa ladan gaɓen da ake ba su, kuma su kiyaye musu fasaha. Wannan abu ne mai yiwuwa ƙarƙashin tsarin da su ke kira YouTube Partnership Program (YPP) wanda ta nan ne ake bada ladan gaɓen nan.

Hakan zai sa a  ɗaga likkafar harkar finafinan Hausar tamu zuwa mataki na gaba.  Akwai hukumomi irin na senso a duniya da su ka yi wa mutanen su irin wannan gata. Me zai hana senso ta Kano ta bi sahu? Su kuma masu shirya finafinan Kannywood, ya kamata su zama masu mutunta al’ummar da su ke cikin su. Addini da al’ada su ne gaba. Ladabi da biyayya na biye. Natsuwa da hankali su ne cikon ginshiƙan nasara a kowanne lamari.  

Wajibi ne kowanne mai shirya fim ya sauke nauyin da ke wuyan sa na biyan hukuma kuɗin haraji da girmama shugabanni. Ba daidai ba ne ka ci moriyar ganga ka yada kauren. Biyan haraji na daga cikin alamun kishin ƙasa. Yi wa shugabanni biyayya inda ta dace wajibi ne ga kowanne ɗan ƙasa nagari. 

Gyara kayan ka dai bai zama sauke mu raba ba! Malam Ɗanladi Z. Haruna marubuci ne kuma masanin intanet da ke zaune a Kano. I-mel:danladiharuna@gmail.com

%d bloggers like this: