Muhammadu Sanusi II ya nuna damuwarsa ga ƙaruwar tamowa a Najeriya

  • Home
  • Labarai
  • Muhammadu Sanusi II ya nuna damuwarsa ga ƙaruwar tamowa a Najeriya

Tsohon sarkin Kano Muhamma Sanusi II ya nuna damuwarsa ga ƙaruwar tamowa a Najeriya. Ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata a Kaduna, yayin taron shekara karo na 50 na ƙungiyar masu yaƙi da tamowa.
Muhammadu Sanusi II wanda Farfesa Hafizu Abubakar ya wakilta ya bayyana damuwar tsohon sarkin a kan wannan matsala.

“Ya damu da yadda alƙaluman masu fama da tamowa ke ƙara yawa a ƙasar, wanda hakan ba abin jin daɗi ba ne.

”Alƙaluman wani lokacin na sauka ko kuma su tsaya a yadda suke, wanda hakan abin takaici ne da ba za a lamunci hakan ba.

”Fatanmu shi ne wannan babban taro zai kawo hanyoyin da za a magance waɗannan matsaloli.” A cewarsa.

Tags:
%d bloggers like this: