Majalisar wakilan Najeriya na ganawar sirri tare da shugabannin hukumomin tsaro.

  • Home
  • Labarai
  • Majalisar wakilan Najeriya na ganawar sirri tare da shugabannin hukumomin tsaro.

Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Wase ya jagoranci wata ganawa ta musamman da masu ruwa da tsaki a kan harkar tsaron ƙasar nan. Taron an fara shi da rana a yau Litinin, 16 ga watan Nuwamba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Manyan jami’ai daga hedkwatar tsaron rundunar sojin Najeriya da rundunar sojin sama da rundunar sojin ruwa da rundunar yan sandan Najeriya, da rundunar tsaro na farin kaya (DSS), sai hukumar kula da shige da fice na ƙasa da kuma hukumar gyaran halayya ta ƙasa duk sun kasance a gurin taron.


Tattaunawar ba za ta rasa nasaba da yanayin tsaron ƙasar da yake ƙara ta’azara. Rahotanni sun bayyana an buƙaci ‘yan jarida da jama’a su fita daga ɗakin taron.

Tags:
%d bloggers like this: