Jam’iyar PDP Ce Mafi Nagarta A Najeriya-Atiku Abubakar

  • Home
  • Labarai
  • Jam’iyar PDP Ce Mafi Nagarta A Najeriya-Atiku Abubakar

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyar adawa ta PDP a zaben shugaban kasa da ya gabata a Najeriya Atiku Abubakar, ya yi ikirarin cewa jam’iyyarsu ta PDP ce mafi nagarta a ƙasar.

Atiku wanda ya taba zama mataimakin shugaban kasa a jam’iyar PDP ya ce ya kamata dukkanin ɓangarorin siyasar Najeriya su zama ƙarƙashin shugabancinta “saboda ita ce jam’iyyar da ta yi amanna da dorewar Najeriya”.

Ya yi wannan furuci ne a saƙon Twitter da ya wallafa a shafinsa.

“Jam’iyyar PDP na da ayyukan da za ta yi a lungu da sako na Najeriya kuma ina shawartar dukkanin ‘yan Najeriya daga bangarori da su yi amanna da PDP, wadda ta yi amanna da dorewar Najeriya,” in ji tsohon mataimakin shugaban kasar. Ana ganin ya yi wannan furuci ne saboda abubuwan dake faruwa a jam’iyar ta su na shirin zaben sabon shugaban jam’iyar da hasashen da ake na wani gwamna zai tsallake ya bar jam’iyar

%d bloggers like this: