Gwamnatin Buhari Na Cike Da Barayi: Sanata Ali Ndume

  • Home
  • Labarai
  • Gwamnatin Buhari Na Cike Da Barayi: Sanata Ali Ndume

Fitatcen Sanata Ali Ndume wanda yake wakiltar Mazabar Borno ta Kudu ya suka sosai ga gwamnatinsu ta APC karkashin Muhammadu Buhari, inda ya ce barayi na cin amanar Shugaban kasar, domin su ne mafiya yawa a gwamnatinsa.

Sanata Ali Ndume

Sanatan ya yi wannan magana ce a cikin shirin Sunday Politics na kafar Channels TV, ya ce akwai mutanen dake yi wa gwamnatinsa zagon ƙasa.

Da aka tambaye shi ko maki nawa zai bai wa gwamnatin jam’iyyarsu ta APC bayan shafe shekara biyar a kan mulki, bai iya bada amsa ba illa ya ce: “Magana ta gaskiya ba na jin daɗin yadda gwamnatin nan ke tafiya.

“Babban abin baƙin ciki shi ne, akwai abubuwan da suke faruwa waɗanda bai zama dole sai sun faru ba. Sau uku muna ƙoƙarin ɗaura shugaban ƙasa (Buhari) a kan mulki ba mu yi nasara ba, amma muka yi nasara a karo na uku.

“Na san Buhari mutumin kirki ne dake son cigaban talakawa. Sai dai ɓarayi ne suka mamaye gwamnatin, abin da ya sa suke cin amanar tsare-tsaren da yake so ya gudanar.”

%d bloggers like this: