Zanga Zangar EndSARS: Kotu Ta Bada Umarnin A Binciki Aisha Yesufu Da Muƙarrabanta

  • Home
  • Labarai
  • Zanga Zangar EndSARS: Kotu Ta Bada Umarnin A Binciki Aisha Yesufu Da Muƙarrabanta

Rundunar yan sanda a Abuja za ta binciki Sam Adeyemi na cibiyar Daystar Christian Centre, da Aisha Yesufu da wasu mutanen da suka taka rawa a zanga-zangar EndSARS.

Wannan ya biyo ƙarar da aka shigar a wata kotu kan mutanen da suka assasa zanga-zangar EndSARS, wanda ta juyo zuwa rikici da ƙone-ƙone da ta jawo asara rayuka da dukiyoyi masu yawa.

Wata kotun majistare dake Abuja ce ta umurci rundunar yan sanda a birnin tarayya da ta binciki al’amarin EndSARS da ake zargin Sam Adeyemi, Aisha Yesufu da sauransu da hannu a ciki.

An bada wannan umarni ne ga kwamishinan yan sandan birnin tarayya, Bala Ciroma, wanda zai jagoranci wannan bincike, kamar yadda jaridar The Cable ta ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamba, ta ruwaito.

Kotun ta ba wa Kwamishinan tsawon makonni biyu da ya kammala bincikensa sannan ya gabatar mata da rahoto, kafin ta yanke hukuncinta.

%d bloggers like this: