Musa Ya Ƙalubalanci Gogewar Mai Horar Da ‘Yan Wasan Super Eagles

  • Home
  • Labarai
  • Musa Ya Ƙalubalanci Gogewar Mai Horar Da ‘Yan Wasan Super Eagles

Mai horar da ƙungiyar kwallon ƙafa ta Kano Pillars, Ibrahim Musa ya ƙalubalanci kwarewar mai horar da ƙungiyar Super Eagles, ɗan asalin ƙasar Jamus, Gernot Rohr kan gazawarsa wajen kare kwallaye huɗu da Najeriya ta zuba a ragar Leone Stars ta ƙasar Sierra Leone a ranar Asabar.

Zakarar kofin kwallon ƙafa ta Afirka karo uku ta kasa kare kwallaye har huɗu da ta zira a ragar Leone Star, wanda ‘yan Najeriya na ji na gani aka dinga farke kwallayen har sai da suke goge su gaba ɗaya. Hakan ya sa Najeriya ta yi kunnen doki 4-4, da Sierra Leone a wasan da aka buga na ƙoƙarin shiga gasar kofin kwallon ƙafa na Afirka (AFCON 2021).

An buga wannan wasa ne a filin kwallo na Samuel Ogbemudia da yake birnin Benin, a Najeriya.

Wannan rashin cikakkiyar nasara ta sa masana kwallon ƙafa yin sharhi kan yadda Najeriya ba ta taɓuka abin arziƙi da ƙasar da ake ganin ba tsaranta ba ce. Ibrahim Musa ya ce lokaci ya yi da ya kamata a sake duba kwarewar mai horar da ‘yan wasan Najeriya Rohr.

Musa ya tuna wani lokaci a baya da mai horarwar, ɗan ƙasar Jamus ya ƙalubalanci mai horarwar Kano Pillars a lokacin da suka yi rashin nasara makamanci wannan, a wasan ƙarshe na Kofin Aiteo a hannun Rangers, inda ya nuna rashin kwarewa da gogaggun ‘yan wasa suka jawo rashin nasarar.

“Na tuna lokacin da muka yi rashin nasara a hannun Rangers a kofin Aiteo 2018, Gernot Rohr wanda ya kalli wasan ya alaƙanta rashin nasarar da rashin kwarewa.

“Ya kuma ce bai ga wani kwararren ɗan wasa a cikin ƙungiyar ba, duk da cewar a lokacin muna Junior Lokosa, ɗan wasan da ya fi kowa yawan kwallaye a NPFL.

“Ya zama wajibi a kwankwasa kwarewar Rohr, yadda ƙungiyar Super Eagles ta yi abin kunya, duk da cewa sune suka fara cin kwallaye huɗu.

“Yaya kwarewar mai horarwar Super Eagles take, tun da ya kasa yin nasara, bayan damar da ya samu ta tazara mai yawa tsakaninsa da ƙungiya kamar Leone Star?” Ya tambaya cikin shaguɓe.

Musan ya ƙara da cewa lokaci ya yi da ya kamata a gayawa Rohr ya fara waiwayar ‘yan wasa da suke wasanninsu a ƙungiyoyin gida.

Ya bada misali da zakaran kofin Afirka 2013 (AFCON) a South Africa, Sunday Mba da yake wasansa a gida, wanda yanzu da wuya ake ba wa masu wasa a gida irin wannan dama.

%d bloggers like this: