Kullum Sai Shifting Post Ake Yi: Yaudarar Ta Isa Haka

  • Home
  • Tsokaci
  • Kullum Sai Shifting Post Ake Yi: Yaudarar Ta Isa Haka

Baba Bala Katsina

  • Idan aka nada ministoci, abubuwa zasu setu. Aka kuwa nada ministoci, sai abubuwa suka yamutse
  • Aka ce idan aka yi budget, abubuwa zasu gyaru. Ai bajet ne bai fara aiki ba. Aka yi bajet, shuru kake ji.
  • Wasu ne a cikin govt, musamman yan majalissa, suke ma mutumin nan zagon kasa, sune suka hana ruwa gudu. Aka zo zabe aka kada mutanen nan, abubuwa basu canja ba, sai ma rikirkicewa suka yi
  • ai kasar ta zama cima zaune, idan aka rufe boda, za’a yi noma, a samu aikin yi, sannan kuma a rage insecurity. Aka bi aka garkame ko ina. Abubuwa suka ida rikicewa. Farashin abinci da kayan masarufi suka kara yi tashin gwaron zabo, insecurity a yankin mu ya karu matuka.
  • aka ce sai an janye tallafin man fetur sannan za’a samu kudin yin ayyukan raya kasa. Aka janye kudin tallafi, amma shi talaka karin farashin mai with its multiplier effects kawai yake gane
  • ASUU na strike an ce babu kudin da za’a gyara ilimi. Kuma ba’a gyara asibiti ba, ba’a samu tsaro ba, ba’a samu aikin yi ba, ba’a samu saukin rayuwa ba ta ko ina Saboda babu kudi. To ko ina kudin kasar suke tafiya, oho!

A gefe daya kuma, haraji kawai ake karawa ana ce ma yan kasa suyi hakuri su biya, dadi na nan gaba. Duk wata kafa da suke shan iska, an kara mata kudi

Wannan dai ya nuna mutanen basu da wata idea na yadda zasu iya fidda kasar nan cikin matsalolin da take ciki. Yanzu abunda ya rage shine mu koma ma Allah, mu roke shi ya kawo mana sauki sannan kuma mu hankalta akan kuskuren da muka yi a baya na zabar mutane da kan su kadai suka sani. In dai su sun ji dadi, dasu da iyalin su, kuma an yi masu hoto, to komi yayi daidai.

Allah dai ya bamu mafita. Amma wannan promises na za’a ji dadi nan gaba, duk maganar yan siyasa ce.

Amma dai dan Arewa ke mulki, dole mu nuna goyon baya. Ko ana yankan naman mu ana gasawa, cewa aka yi muyi shuru, mu ce daidai ake yi.

Daga Baba Bala Katsina

%d bloggers like this: