Hadimin Shugaban Kasa Ya Karyata Biyan ‘Yan Tubabbun ‘Yan Boko Haram Alawus 150, 000

  • Home
  • Labarai
  • Hadimin Shugaban Kasa Ya Karyata Biyan ‘Yan Tubabbun ‘Yan Boko Haram Alawus 150, 000

Hadimin shugaban kasa kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa gwamnatin Muhammadu Buhari na shirin fara biyan tubabbun ‘yan Boko Haram naira 150,000 a duk wata.

Rahotanni da wasu kafofi yada labarai suka saki ya nusa gwamnatin Najeriya na biyan tubabbun ‘yan Boko Haram albashi N150,000 a wata, watakila don a kawar da zuciyarsu daga komawa inda suke fito.

Sai dai Bashir Ahmad, ya ce wannan labarin kanzon kurege ne. Hadimin shugaban kasan ya yi kira ga yan Najeriya da su yi watsi da irin wadannan labarai.

Ahmad ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita. Yace: “Gwamnatin tarayya ba ta shirin fara biyan tubabbun yan Boko Haram kudi N150,000 a wata.”

“Labari ne maras asali kuma na bogi.” Ya kara da cewa.

%d bloggers like this: