Farashin Man Fetur Ya Karu A Najeriya

A yayin da ake kokun tsadar rayuwa da lalacewar tattalin arziki, shi ma farashin man fetur ya tashi a fadin duniya. Hakan ya sa a Najeriya ma farashin zai tashi, saboda sabon farashin jigilar mai a Depot da kamfanin PPMC ya samu kari daga N147.67 zuwa N155.17, wannan labari Premium Times ce ta ruwaito shi.

Kamfanin PPMC wani sashe ne na kamfanin man feturin Najeriya (NNPC), wanda suke shigo da kusan dukkan man feturin da ake amfani a kasar. Farashin man yanzu na iya tashi zuwa N170 lita a gidajen mai. A takardar da kamfanin ya saki ranar 11 ga Nuwamba, an fahimci cewa za a fara sayar da mai a wannan farashin ranar 13 ga Nuwamba, 2020.

Wannan takardar Ali Tijjani na PPMC ya rattabawa hannu, kuma ya nuna cewa kudin shigo da tattacan mai daga kasar waje ne ya hau daga N119 a Satumba zuwa N123 a Nuwamba.

Hakazalika, farashin mai a Depot ya tashi daga N138 a Satumba, zuwa N142 a Nuwamba, 2020. Yanzu haka, farashin Depot ya tashi zuwa N155.17.

Farashin Depot shi ne farashin da ake sayarwa ‘yan kasuwa man fetur, sannan su sanya nasu farashin kafin sayarwa ga yan kasa.

%d bloggers like this: