Rundunar Sojoji Ta Sake Yunƙurin Neman Shekau Ruwa A Jallo

  • Home
  • Labarai
  • Rundunar Sojoji Ta Sake Yunƙurin Neman Shekau Ruwa A Jallo

Rundunar sojojin Najeriya ta sake fitar da sunayen ‘yan ta’adda 86 da take nema ruwa a jallo. Wannan shi ne karo na huɗu da aka fitar da irin waɗannan sunaye.

An fitar da sunayen yayin bikin ƙaddamar da ‘yan aikin sa kai na tsaro (CJTF) da aka yi a sansanin soji a Chabal.

Gwamnan Borno Farfesa Babagana Zulum da shugaban hafsan sojojin Najeriya Janar Tukur Burtai ne suka ƙaddamar da wannan ƴunƙuri tare da gabatar da sunayen waɗanda ake nema.

Daga cikinsu ‘yan ta’addan da ake nema akwai: Abubakar Shekau, da Abu Mus’ab Al-Barnawi da Modu Sulum da Umaru Tela da Imam Balga da Abu Umma da Malam Bako (Hisbah) da Abu Darda da Ibrahim Abu Maryam da sauransu.

Babban hafsan sojojin ya ce. “Muna neman cikakken haɗin kan jama’a da masu aikin sa kai na tsaro. Za a rabawa kowa kwafi don bibiya.”

Ya ƙara da cewa. “Wasu wataƙila na tare da ku, suna kai komo a kasuwanni da sauran gurare. Dole ne a tsamo su tare da waɗanda ke jeji. Idan kun yi arba da su, ku tabbata kun ci ƙaniyarsu idan har ba za su yarda a tsare su ko a kama su ba.”

Shugaban hafsan sojojin ya godewa gwamnan Borno saboda gudunmawarsa wajen samar da kayan aiki da haɗin kai ta kowacce fuska.

Ya kuma yabawa masu aikin sa kan, inda ya bayyana ƙoƙarin da rundunar sojojin ta fara na ɗaukar ‘yan sa kan cikin rudunar sojojin Najeriya.

%d bloggers like this: