Gwamnati Na Ƙoƙarin Haɗa Kan Kungiyoyin Ma’aikatan Jami’oi, ASUU, NASU, NAAT Da SSANU

  • Home
  • Labarai
  • Gwamnati Na Ƙoƙarin Haɗa Kan Kungiyoyin Ma’aikatan Jami’oi, ASUU, NASU, NAAT Da SSANU

Gwamnatin tarayya ta fara yunƙurin ganin ta haɗe kan ƙungiyoyin ma’aikatan jami’oi a matsayin wata lema guda ɗaya. Hakan ya fito ne daga bakin Babban Sakataren hukumar jami’oi ta Najeriya (NUC), Farfesa Abubakar Adamu Rasheed.

A cewarsa, rabe-raben ƙungiyoyin ma’aikatan jami’a ya sa kowaccce ƙungiya na bijiro da nata buƙatun a ɗaiɗaiku, wanda hakan na kawo tsaiko wajen gwamnati ta biya musu buƙatunsu.

Raheed ya alaƙanta hakan da babban dalili da ya sa tsarin jami’a a Najeriya ba zai iya yin kafaɗa da takwarorinsa dake ƙasashen ƙetare a inganci ilimi.

Babban sakataren ya yi wannan jawabi ne a matsayin babban baƙo a taro karo na biyu na Quadrennial National Delegates da ƙungiyar manyan ma’aikatan jami’a (SSANU) ta shirya a ranar Litinin a Abuja.

Ya ƙara da cewa, suna kan tautaunawa da shugabancin ƙungiyar kwadago ta ƙasa, yadda za ta gaiyaci dukkanin ƙungiyoyin ma’aikatan jami’oi don tattaunawa, tare da fahimtar mihimmancin zama a ƙarƙashin lema ɗaya.

Ƙungiyoyin da ake sa ran za su kasance cikin wannan yunƙuri sun ƙunshi ƙungiyar malaman jami’oi ta Najeriya ASUU da ta ma’aikatan jami’oi marasa koyarwa NASU da ƙungiyar ma’aikatan jami’oi masu kula da ɗakunan gwaje-gwaje NAAT sai kuma ƙungiyar manyan ma’aikatan jami’oi SSANU.

A bayaninsa ya nuna amfanin ƙungiyoyin su shiga dunƙulalliyar yarjejeniya da gwamnati, maimakon a rarrabe.

Abubakar Rasheed ya koka yadda akoyaushe ƙungiyoyin da gwamnati ke tada jijiyoyin wuya kan walwalar ma’aikata, wanda a ƙarshe ɗalibai ne ke cutuwa.

Ya ce, “Babu wata jami’a a duniya da za ta gudana yadda ya kamata a keɓance. Abin takaici ne yadda ƙungiyoyin NAAT da ASUU da SSANU suka raba kan jami’oi, kowacce ƙungiya na neman abubuwa daban-daban.

”A mafi yawancin lokaci, a sanda da wata ƙungiya ke tattaunawa da gwamnati, a lokacin ne sauran ƙungiyoyi za su sa ɗambar yajin aiki har sai an biya musu buƙatunsu.” Ya ce.

Babban sakataren ya faɗi cewa Minstan Ilimi, Adamu Adamu ya samu sahalewar shuguban ƙasa Muhammadu Buhari na ya tura wani kwamiti da zai ziyarci dukkan jami’oin Najeriya mallakar gwamnati.

Ya ce hakan ya biyo bayan abin rashin jin daɗi da ya faru a Jami’ar Lagos, inda Kwamitin Zartarwar Jami’ar ƙarƙashin jagorancin Pro-Chancellor, Wale Babalakin suka zartar da korar tsohon shugaban jami’ar, Oluwatoyin Ogundipe.

A cewarsa za a ƙaddamar da wannan kwamitin nan ba da jimawa ba don su zagaya jami’oi tare da kawo rahoton shekara goma, wanda za a kasa gida biyu na tsawon shekaru biyar-biyar kowanne.

%d bloggers like this: