Gwamnatin Katsina Ta Kashe Miliyoyin Kuɗi Wajen Gyaran Filayen Wasanni

  • Home
  • Wasanni
  • Gwamnatin Katsina Ta Kashe Miliyoyin Kuɗi Wajen Gyaran Filayen Wasanni

A ranar Laraba ne gwamnatin Katsina ta sanar da kashe naira miliyan 175.5 wajen gyaran filayen wasanni guda biyu tare da ɗaga darajarsu a jihar.

Kafar sadarwa ta Katsina Post ta ruwaito cewa, kwamishinan wasanni da cigaban jama’a na jihar Sani Danladi, ya sanar da kashe naira miliyan 111.3 a wajen ɗaga darajar filin wasa na Malumfashi Township Stadium, sai kuma naira miliyan 64.2 a wajen ƙarasa aikin gyaran filin wasa na Township Sport Complex dake cikin Katsina.

“Wannan zai taimaka wajen bunƙasa harkokin wasanni tsakanin matasa a jihar.” Inji kwamishinan.

Ya ƙara da cewa an kashe naira miliyan 9.25 wajen yin magani ga mahaukata da kwashe su daga tituna. Sannan an kashe naira miliyan 1.57 wajen mayar da ‘yan gudun hijira matsugunansu a gida da wajen jihar.

%d bloggers like this: