Kotu Ta Tura Naziru Sarkin Waƙa Gidan Yari

  • Home
  • Labarai
  • Kotu Ta Tura Naziru Sarkin Waƙa Gidan Yari

A yau Laraba ne wata kotu a Kano ta soke wani beli da aka taɓa sakawa mawaƙi Nazir Ahmed Sarkin Waƙa, a inda ta sake gindaya masa sababbin sharuɗdan beli.

Za a iya tunawa a watan Satumba, 2019 aka fara kama mawaƙin Nazir, wanda daga bisani kotun majistere ta sake shi, bayan ya cika sharuɗɗan beli a wannan lokaci.

Kafa waɗannan sababbin sharuɗɗan beli ya sa mawaƙin bai iya cika su ba akan lokaci, wanda hakan ya sa Alƙalin kotun tasa ƙeyarsa zuwa gidan gyaran hali.

Rahotanmu ya binciko cewa an kafa waɗannan sharuɗɗan belin a yau Laraba, wanda dole sai an samu jinkiri kafin a cika ƙa’idojin da aka saka cikin ƙanƙanin lokaci.

Tura shi gidan yarin ya biyo bayan zarginsa da hukumar tace finafinai take na ya saki wata waƙa ba tare da an tantance ta ba.

Sharuɗɗan sun haɗa da kawo wani Maigari da zai tsaya masa da kuma Kwamandan Hizbah na ƙaramar hukuma a matsayin sharuɗɗan beli.

%d bloggers like this: