Rahama Sadau Ta Yi Nadama

Jaruma Rahama Sadau ta yi nadama tare da neman afuwar jama’a bisa wasu hotunanta da ta saki, wanda suka dinga janyo mata Allah wadai a faɗin duniya.

Jarumar ta yi wani gajeren rubutu tare da sakin wani faifan bidiyo a account ɗinta na Instagram.

Ga abin da take cewa:

Na yi wannan video din ne cikin nadama da takaici. Ina kuma mai ba da hakuri bisa abin da ya faru ga dukkanni Hausawa, abokan aikina da musulmai baki daya bisa wannan hoto nawa da ya jawo wannan cece-ku-ce.

Wannan ba dabi’a ta ba ce a matsayina ta musulma. Ni masoyiyar Manzon Allah (SAW) ce, kuma Ina yaqi da duk wani wanda ya taba shi ko ya taba addinina. Kaddara ce ta kawo kawo har wani yayi batanci akansa Akan hotona. BANA TARE DASHI, Allah kuma ya la’ance shi Akan wannan batanci da husuma daya tayar a Lokacin da duniya ke cikin wani Hali . Haka ba zai kara faruwa a kai na ba insha Allah.

Na gode Allah ya kare mana imanin mu da addinin mu.

Rahama Sadau❤️

%d bloggers like this: