Ɗan Wasan Najeriya Ahmad Musa Ya Bar Ƙungiyar Al-Nassr Ta Saudiyya

  • Home
  • Wasanni
  • Ɗan Wasan Najeriya Ahmad Musa Ya Bar Ƙungiyar Al-Nassr Ta Saudiyya

Shahararren ɗan wasan Najeriya Ahmad Musa ya bar ƙungiyar Al-Nassr ta Saudiyya, bayan ya kwashe shekara biyu yana taka musu leda.

Ƙungiyar ta bayyana labarin tafiyar ɗan wasan a shafinta na Twitter. A shekara biyu da ya yi da ƙungiyar, ya jefa mata kwallaye 11 a wasanni 58 da ya buga, sai kuma taimakawa a ci kwallaye har 14, tare da taimaka mata ɗaukar kofin gasar ƙasar da kuma Super Cup.

Kafar BBC Hausa ta ruwaito cewa, Musa mai shekara 28 yanzu ba shi da wata ƙungiya sai dai rahotanni na cewa yana son koma wa Turai ne da taka leda bayan barin ƙungiyar cikin ruwan sanyi.

A wani saƙo da ƙungiyar ta wallafa, tare da haɗa wani hoton bidiyo tun daga farkon zuwansa har da ƙwallayen da ya jefa, ƙungiyar ta yi masa fatan alheri a rayuwar ƙwallonsa a nan gaba.

“Mun gode tauraron Najeriya muna maka fatan alkhairi a rayuwarka ta gaba Ahmed Musa!,” Ƙungiyar Al Nassr ta wallafa.

Tsohon ɗan wasan Kano Pillars ya taɓa taka leda a ƙasar Rasha da ƙungiyar da ya yi zaman aro na shekara biyu CSKA Moscow, wanda ya koma Al Nassr kan kwantaragin shekara huɗu daga Leicester City.

%d bloggers like this: