Me ya sa ƙungiyar ASUU ba ta janye yajin aiki ba?

  • Home
  • Labarai
  • Me ya sa ƙungiyar ASUU ba ta janye yajin aiki ba?

Ƙungiyar malaman jami’oin Najeriya (ASUU) dake cikin yajin aiki ta bayyana cewa tana jira ne gwamnati ta yi gwajin tsarin biyan kuɗi na UTAS ne da suka miƙa musu. Ƙungiyar ta ASUU ta samar da UTAS ne bayan ta ƙi amincewa da IPPIS ta gwamnatin tarayya ta samar a matsayin hanyar biyan albashi.

A zaman da ƙungiyar ta yi a baya da gwamnati an samu fahimtar juna, amma kuma ƙungiyar ta ASUU ta ƙi amincewa da tsarin da za a biya su kuɗin kafin a zartar da amfani da UTAS, domin gwamnati ta nemi su shiga tsarin IPPIS kafin a gama gwajin wanda suka samar, sai dai sun ƙi amincewa da hakan.

Hakan ya sa ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta ce har yanzu ba ta janye yajin aikin da take yi ba saboda tana jira gwamnati ta yi gwaji kan tsarin biyan albashi na UTAS.

Shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi a wata hira da ya yi da jaridar The Punch ya ce akwai buƙatar gwamanti ta bawa hukumar NITDA dama yin gwaji kan UTAS.

Ya ce, “NITDA ce za ta yi gwajin, gwamnati ne za ta bada izinin yi don NITDA hukuma ce a ƙarƙashin gwamnati kuma sai ta samu izini za ta yi gwajin.”

Shugaban na ASUU ya ƙara da cewa, “Har yanzu muna magana, mun sanar da su matsayar mu, muna tunanin za mu gana wannan makon idan ba su canja tsarinsu ba. An ɗage taron ranar Litinin. Sun amince da UTAS sun kuma ce mu tafi muyi gwaji a bangaren mu, mun fara aiki. Mun gabatar wa ɓangarori uku UTAS, ma’aikatar ilimi, shugaban majalisar dattawa da jami’an ma’aikatar kuɗi da ofishin akanta janar inda dukkan masu ruwa da tsaki ciki har da NITDA suka hallarta. Idan gwamnati ta amince da shi ba wani abu da zai ɗauki lokaci bane.”

Ogunyemi ya kuma yi bayyani cewa a shirye suke su koma aiki, matuƙar gwamnati ta shirya yin abin da ya kamata.

“Mambobin mu a shirye suke su koma aiki idan har gwamnati za ta yi abin da ya dace a bangarenta. Ina fata ba ka nufin mambobin mu su koma aiki tare da yunwa a cikinsu ko kuma a janye yajin aikin ba tare da wani ƙwaƙwaran mataki daga ɓangaren gwamnati ba. Ba son yajin aikin mu ke yi ba, don ɗaliban ‘ya’yanmu ne.”

Shugaban ya ƙara da cewa. “A halin yanzu ba mu ga dalilan da zai sa mu yarda cewa gwamnati za ta yi abin da take faɗa mana ba, amma da zarar mun ga alamar da gaske su ke yi, za mu fada wa ‘yan Najeriya.”

%d bloggers like this: