Batanci Ga Musulunci: Ɗan Wasa Pogba Ya Daina Takawa Faransa Leda

  • Home
  • Wasanni
  • Batanci Ga Musulunci: Ɗan Wasa Pogba Ya Daina Takawa Faransa Leda

Sakamakon cin mutunci da ɓatanci ga addinin musulunci, ɗan wasan Faransa Paul Pogba ya dakatar da taka leda ga ƙasarsa ta Faransa.

Pogba mai shekaru 27 na taka leda ne a Manchester United.

Ya yanke wannan hukunci ne sakamakon kalaman shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron wanda ya zargi addinin musulunci da ta’addanci.

Rahoton daina bugawa Faransa leda a ɓangaren Pogba ya fito a jaridun gabas ta tsakiya. Duk da cewa ba a ji ɗan wasan Paul Pogba ya ƙaryata ba.

A wannan lokaci wasu shugabannin duniya sun yi Allah wadai da kalamin Macron. Ko shugaban ƙasar Turkey ya ce Emmanuel Macron ya buƙatar a binciki kwakwalwarsa.

%d bloggers like this: