Wanda suka shirya zanga-zangar SARS sun ce a koma gida

  • Home
  • Labarai
  • Wanda suka shirya zanga-zangar SARS sun ce a koma gida

Wata gamayyar ƙungiya ta Feminist Coalitiin da suke da hannu wajen shirya zanga-zangar #EndSars, sun nemi matasa su haƙura da zanga-zanga su koma gida.

Ƙungiyar ta sanar da hakan a shafinta na Tuwita, wasu awanni bayan shugaban ƙasa ya yi jawabi akan rikicin da mataken da gwamnatin tarayya ta ɗauka.

Ƙungiyar ta sanar da cewa ta dakata da karɓar gudunmawa, wanda suka dinga karɓa a faɗin duniya a tsawon kwanaki don ganin sun cimma manufar da suka sa gaba. Ƙungiyar ta sanar da ta tara kuɗi har dalar Amurka 400,000 wanda har yanzu ba a kashe su ba.

Ga alama wannan sanarwa za ta kawo ƙarshen wannan zanga-zanga, duba ga yadda bayanai suke fitowa na rashin tunani da ƙona dukiyoyin da asarar rayuka da aka yi.

Bincike da ake gudanarwa a mataki daban-daban zai ƙara bada haske na wanda suke da hannu kan wannan aika-aika, da yadda za a yi maganinta gaba ɗaya.

Daga

Zadeen Kano

%d bloggers like this: