#EndSARS An ƙone motocin mutane a Abuja

Zanga-zangar #Endsars na sauya salo iri-iri, musamman a birnin tarayya Abuja. Ana zargin wasu ɓata gari na amfani da wannan zanga-zangar don cimma wata manufa ta daban.

Yayin da ake gabatar da zanga-zangar, wasu kan yi amfani da wannan dama wajen farma jama’a tare da lalata dukiya.

A yau hakan ce ta faru a birnin tarayyar, inda wasu matasa ɗauke da makamai suka kai hari tare da ƙone motocin jama’a.

A taro irin wannan, wasu na zuwa gun zanga-zangar don samun damar sajewa da jama’a, domin cimma wata manufa ta daban.

Ya zama wajibi gwamnati ta yi ƙoƙarin gano bakin zaren, yadda za a shawo kan matsalar.

%d bloggers like this: