Zanga-Zangar SARS: Mataimakin Shugaban Ƙasa, Osinbajo Ya Nemi Gafarar ‘Yan Ƙasa

  • Home
  • Labarai
  • Zanga-Zangar SARS: Mataimakin Shugaban Ƙasa, Osinbajo Ya Nemi Gafarar ‘Yan Ƙasa

Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya nemi gafarar ‘yan ƙasa game da “jan ƙafar da gwamnati ta yi akan gyaran ayyukan rundunar ‘yan sandan ƙasar.

Ya nemi wannan afuwa ce a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya ce yana sane da cewa matasa na cikin fushi game da abin da rundunar SARS ta aikata, “kuma suna da dalilin yin hakan”. Sanarwar ta ce.

Ya ƙara da cewa, “Ya ku ‘yan Najeriya, na sani cewa da yawa daga cikinku ransu a ɓace yake, cewa ya kamata a ce mun ɗauki matakai cikin sauri. Saboda haka muna neman afuwarku.”

A ranar Alhamis ne mataimakin shugaban ƙasar ya jagoranci zaman Majalisar Tattalin Arziƙin Najeriya mai ɗauke da wakilcin gwamnoni da ministan Abuja, wanda majalisar ta yanke wasu matakai da za su bi, kamar yadda masu zanga-zanga suka buƙata.

Osinbajo ya ce: “Na sani sarai yadda matasa ke ji. Da yawa na jin cewa mun yi gum da bakimmu kuma ba mu yi komai ba. Kuna da dalilin yin hakan.”

“Tun daga makon da ya gabata, muna bin zanga-zangar kuma na yi tattaunawa da masu ruwa da tsaki da ya kamata ku sani. Gaskiya na ɗaya daga cikin rukunan gudanar da mulki.”

Daga cikin matakan da Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa ta ɗauka, akwai kafa kwamitocin bincike a kowacce jiha da za su zaƙulo waɗanda ‘yan sanda suka ci zarafi “domin yi musu adalci”.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce “na san burinku shi ne ku gani a ƙasa kuma ina faɗa muku cewa ana tsaka da yin aiki.”

Wajibi ne kowacce jiha ta kafa kwamitin shari’a domin binciken cin zarafi da ‘yan sanda suka aikata wanda zai kasance ƙarƙashin shugabancin:

-Tsohon alƙalin kotun tarayya
– Wakilai biyu daga ƙungiyoyin farar hula
-Ɗan sanda ɗaya mai ritaya
– Wakilin matasa guda ɗaya
– Wakilin ɗalibai guda ɗaya
-Wakilin antoni janar na jihar guda ɗaya
-Wakili guda ɗaya daga Hukumar Kare Haƙƙi ta Ƙasa

Aikin kwamitin

-Karɓa tare da bincika ƙorafin cin zarafi ko kisa da ‘yan sanda suka aikata
-Tantance shaidu da aka gabatar tare da tabbatar da gaskiyarsu
-Bayar da shawarar biyansu diyya da kuma matakin gyara da za a iya ɗauka

-Kwamitin zai gudanar da aikinsa ne cikin wata shida *sai dai idan gwamna na da wani ƙwaƙƙwaran dalili na tsawaita shi

Majalisar ta umarci kowanne gwamna da ya kafa wata gidauniya mai suna Victims Fund da za ta biya waɗanda aka ci zarafi diyya.

%d bloggers like this: