Za A Wajabtawa ‘Yan Najeriya Mallakar Lambar Katin Ɗan Ƙasa

  • Home
  • Labarai
  • Za A Wajabtawa ‘Yan Najeriya Mallakar Lambar Katin Ɗan Ƙasa

Ministan Sadarwa ta tattalin arziƙi na zamani na Najeriya, Dakta Ali Isa Pantami ya sanar da cewa nan gaba za a wajabta wa ‘yan Najeriya mallakar lambar shaidar ɗan ƙasa ta NIN.

Ministan ya yi wannan jawabin ne yayin da hukumar samar da katin ɗan ƙasa (NIMC) ta kai masa ziyara a ofishinsa dake Abuja.

Ya kuma shawarci hukumar ta ƙara adadin mutanen da ta ke yi wa rajista duk wata daga 500,000 zuwa miliyan 2.5, saboda wahala da ake fuskanta wajen yi wannan katin.
A ƙarshe ya buƙaci hukumar da kafa cibiyoyi a sassan ƙasar ta yadda mutanen ƙasa za su samu kafar kai ƙorafe-ƙorafe na abin da ya shafi kati ko lambar ta NIMC.

%d bloggers like this: