BABBAN ABIN DA YA SA NA SHIGA WANNAN SANA’A, KISHIYA AKA YI MIN- HAJARA SANI SULAIMAN

  • Home
  • Labarai
  • BABBAN ABIN DA YA SA NA SHIGA WANNAN SANA’A, KISHIYA AKA YI MIN- HAJARA SANI SULAIMAN

HAJIYA HAJARA SANI SULAIMAN mace mai kamar maza, domin ta yi fice ne a sana’ar kafinta. Sana’ar da ba kasafai ake ganin mata a cikinta ta ba. Ta Samu shekara ashirin da ɗaya a cikin wannan sana’a, tun tana rarrafe har kamfanin Hajara Furniture ya miƙe.
A wannan tattaunawa da ta yi da wakilin AMON NASARA, NAZIR IBRAHIM KALLAH, ta faɗi abin da ya ja hankalinta har ta shiga wannan sana’a, da irin nasarori da ta samu a dalilin wannan sana’a.

Amon Nasara (AN): Za mu so jin sunan Hajiya?
Hajara Sani Sulaiman (HSS): Sunana Hajara Sani Sulaiman, ina zaune ne a Kawon Majalisa dake Kano.

AN: Tun yaushe kika fara wannan sana’a ta kafinta?
HSS: Gaskiya wannan sana’a na kai shekara ashirin da ɗaya ina yin ta.

AN: Ko kin gaji wannan sana’a ne a gurin magabata?
HSS: Ko ɗaya ban gada ba, kawai na shigeta ne saboda sha’awa, kuma Allah ya taimake ni a cikinta.

AN: Me ya ja ra’ayinka kika shiga wannan sana’a da maza ne suka fi yinta?
HSS: Eh to, abin da ya ja ra’ayina na ga sana’ar rufin asiri ce, kuma maza ne suka fi yin ta ba mata ba. Na yi sha’awar sana’ar saboda ba mata a cikinta.

AN: Sana’a ce mai wahala, shin ko kin samu horo ne, duba ga yadda da kanki kike yin wasu abubuwa?
HSS: Ban samu wani horo ba. Babban abin da ya sa na shiga wannan sana’a, kishiya aka yi min. Bayan an yi min kishiya sai ‘yar uwata ta sayo min kayan gado, wato an yi min sauyin kayan ɗaki. Wannan ya sa mata idan sun shigo suke sha’awar kayan gadon.

To, sai wata da ta ga kayan a gurina ta ce sai na sayar mata. Ni ko na sayar mata da kayan gadon.
Bayan na sayar mata da kayan gadon, sai na yi wa ‘yar uwata magana. Akwai wani bawan Allah da yake sana’arsa ta kafinta akan titin Ibrahim Taiwo. Sai ta haɗa ni da shi. Idan ya bugo kayan ya kawo min, da na sa su a ɗakina mutane suka gani suka yi sha’awa sai na sayar musu. Har Allah ya sa ake kirana ina sayen kayan katakon.


Daga nan sai na fara ajiye kafintoci a gidana. Da na fara ajiye su, idan suna aiki ina gani, har Allah ya sa na iya wasu abubuwa. Daga nan har hannuna ya fara kwarewa, zuwa lokacin da na kware. To ni ba wani horo na je na yi ba akan sana’ar.

AN: Akwai wani banbanci ga ku mata masu wannan sana’a da maza masu yin ta?
HSS: Akwai banbanci, banbancin shi ne mata ba za mu sa tebir a guri mu goge katako ba, idan dai ba wadatatcen guri gareka ba, yadda za ka yi komai a cikin gidanka. Domin a waje ba zai yu ba, ana yi ne a cikin gida. Wani bai san kana yi ba, idan dai ba ‘yan uwanka mata ba da sukan shigo su gan mu muna yi. Tun suna dariya har suka zamo suna sha’awa. Akwai mata da dama da suke yi min aiki, suna ƙarƙashina. Suna min gugar katako lokacin ana jan katako. Akwai waɗanda nake basu suna goge min.

AN: Wane cigaba kika samu a cikin wannan sana’a?
HSS: Alhamdulillah, an samu cigaba sosai tun da ba ka rasa ci ba ko sha ba. Kuma ka samu rufin asiri sosai, tun da ka ga ban taɓa tunanin zan biya kuɗin kujerar Makka da kuɗina. Amma Makka sau biyu ina biya da kuɗina, ina zuwa ina dawo wa.

AN: Yara nawa ne suke cin abinci a ƙarkashinki a wannan sana’a, da waɗanda kika yaye?
HSS: Ba zan iya lissafa maka yaran da suke ƙarƙashina ba, duba ga irin wanda aka yaye, wasu kuma sun yaye kansu sun tafi, wasu kuma tun ba su iya buga kayan ba, amma yanzu sun iya. Wasu ma yara ne, amma sun iya sosai, ba abin da za ka ba wa yaro bai iya shi ba. A gaskiya ba zan iya lissafa maka ba a yanzu.

AN: Duba ga abin da kika faɗa, akwai matasa sosai kenan?
HSS: Wallahi akwai su, kuma tsakaninmu da su sai ban girma.

AN: Me mutum yake buƙata idan yana son shiga wannan sana’a?
HSS: Da farko sana’ar kafinta tana buƙatar haƙuri tare da riƙon amana. Bayan nan za ka nemi kayan aiki da jari. Kayan aiki da za ka buƙata sun haɗa da guduma da fincis da zarto da bar da abin gugar katako. Sai injin Jannareto saboda yanka, ka san sha’anin wutar lantarki babu tabbas.

AN: Kowacce sana’a na da ƙalubale, wane irin ƙalubale ne yake cikin wannan sana’a?
HSS: Akwai ƙalubale, tun da idan ka kai farin wata haske, ba za ka haska duniya ba. Dole za ka samu ƙalubale kalala-kalala na jama’a, na tsangwama, na wani ya dinga ganin ka fiye neman kuɗi ne, duk ba abin da ba a cewa.
Akwai wani mutum da ya taɓa zuwa zai sayi kaya ya same ni. Da yake ba a barin maza su shigo idan muna aiki, amma sai mutumin nan ya faɗo. Shi ne da ya ganni ina aiki yake tambaya ko ni bahaushiya ce. Na ce masa cikakkiyar bahaushiya ce, saboda iyayena duk a nan aka haife su. Na ce ka ga a Dala Makwalla aka haifi mahaifiyata. Amma ya ce bai yarda ba. Na ce to shike nan.

AN: Bayan wannan sana’a ta kafinta, ko kina yin wata sana’a?
HSS: Sana’ar katakon ta fi ƙarfi, sai kamar katifu saboda masu sayan kayan katako. Wani lokacin muna siya da fulillika mu ajiye. Amma ba ni da wata sana’a da ta fice ta kayan katako, ita ta fi ƙarfi.

AN: Kin taɓa samun wani tallafi a gwamnatance don bunƙasa wannan sana’a?
HSS: Wallahi ni ban taɓa samu ba, ko naira biyar. Ko a zo gurina a ga me muke yi.

AN: Kina da wani kira ga gwamnati saboda masu sana’a irin taku da suke riƙe da kansu kuma suke samar da ayyuka?
HSS: Akwai yara da suke wannan sana’a, amma ba su da jari. Akwai mata da yawa da suna so su yi sana’a, amma ba su da yadda za su yi, domin sana’a ce dake buƙatar jari. Domin idan aka zo gurin sana’arka aka ga babu komai, tsoron ba ka aiki ake. Gani ake in an baka aiki cinyewa za ka yi, kuma a ina kuɗin za su fito. Idan hukuma za ta shigo, hakan zai taimakawa al’umma.

AN: Shin akwai mata da yawa da suke wannan sana’a?
HSS: Gaskiya ba mu da yawa, sai dai akwai masu sayarwa da yawa. Amma masu yin aikin ba mu da yawa, tun da ba kowacece za ta iya ɗaukar wannan wahala ba.

AN: Ko akwai ƙungiyar da kuke ta masu wannan sana’a?
HSS: Da mun yi ƙoƙarin kafa ƙungiya, amma ka san abin mata, sai ake ganin kamar kai don kana da ƙarfi ne. Ba za su dubi idan aka tafi a ƙungiyance, ko wani abin alheri zai iya shigowa ba. Gaskiya ba mu da ita.

AN: Mene ne burinki a cikin wannan sana’a?
HSS: Ni dai burina ba zai wuce kullum na ga mutum ya kawo ɗansa ko ya kawo kansa ya koya ba. Shi ne babban burina, saboda na riga na san ni mace ce, wannan abin ba mai ɗorewa ba ne, wata rana dole zan bar shi.

AN: Yaya kike tsara rayuwarki ta aure da kuma aikin wannan sana’a?
HSS: Tsarin aure a haka ake yi, tun da maigida ya yarda kuma yana ɗaya daga cikin masu bada gudunmawa. Sannan akwai yara masu taimakawa, lokacin abinci za su yi, ‘yan share-share da wanke-wanke duk za su yi. Duk wasu al’amuran gidan ana yi, amma ina ƙoƙarin inga idan maigida na gidana na dawo da wuri kafin ya dawo.

AN: Wane lokaci kike fitowa gurin aiki da kuma lokacin da kike tashi?
HSS: Idan akwai aiki da yawa, lokacin ciniki ya buɗe, bakwai na safe za ta yi min a gidan aiki. Wani lokacin ba zan baro gidan ba sai sha ɗaya na dare, wani lokacin goma da rabi na dare. Amma idan aiki ya cunkushe har sha biyu ina kai wa.

AN:Yaya kike samun nishaɗi idan ba a bakin aiki kike ba?
HSS: Yara za su zo a zagaye ni ana hira, har su dinga cewa Umma ba za ki fita ba ne, na ce eh. Akwai nishaɗi sosai tun da za ka zauna, za ka yi baƙi, za ka saurari kowa. Amma idan a gun aiki ne, duk wanda ya zo idan ba akan aiki ba ne, ba lalle za ka saurare shi ba.

AN: Ta ɓangare abinci, wane abinci kika fi so a rayuwarki?
HSS: To, abincin malam Bahaushe ai ba zai wuce tuwo ba, shinkafa sai ɗan wake.

AN: Ta ɓangare sitira, wane nau’in sutura kika fi so?
HSS: Na fi son atamfa, ita ce suturar talaka.

AN: A wannan sana’a za ki haɗu da mata da yawa da za su nemi ku ƙulla alaƙa, musamman gayyata zuwa bukukuwa, duba ga kuna yi musu kayan ɗaki, yaya kike samun lokaci wajen wannan mu’amula?
HSS: Idan ba ni da aiki ina zuwa, amma idan aiki ya cushe sai dai na tura yara, na basu gudunmawa ta, ko kuma na yi waya.

AN: A matsayinki na mace mai wannan sana’a, wacce shawara kike da ita ga mata da suke zaune babu wata sana’a, sai abin da aka ba su?
HSS: Wallahi ka taɓo min inda nake son magana. Domin idan na ga mace a zaune tausayinta nake wallahi, saboda sana’a ta zama dole. Ba komai za ka tausayawa ba sai ran da namiji bai da shi. Amma idan kina sana’a, kin zauna kin nema, to Alhamdulillah.
Amma ki zauna ke ce barci, kina kwance ki yi na safe ki zo ki maimaita na rana. Kullum sai dai ki ci ki kwanta, a gaskiya wannan ba rayuwa ba ce. Ki tashi ki nema, amma wasu matan suna son su yi, matsalarsu a mazan ne, ba sa so. Amma idan an samu haɗin kan namiji, to a bar mace ta fita ta nema. Ko min ƙanƙanta tana juyawa, wata rana sai abin ya baka mamaki.

AN: Kin taɓa samun wani ƙalubale daga maigidanki akan wannan sana’a?
HSS: Ƙalubale ɗaya ne, shi ne daren da ake. Mutum zai ɓata rai, amma ka san yadda za ka yi ka janyo hankalinsa tun da ka san laifi ka yi. Amma wani lokacin har gidan aikin ya kan je ya same ni, ya ga abin da ake. Wani lokacin jikin nawa ga shi nan fenti da ƙura, wani lokacin na kan ce gwanda da ka zo, ka ga ka taimaka.

AN: Mun gode kwarai da lokacinki. Allah ya ƙara buɗi.
HSS: Ameen, ameen. Na gode.

%d bloggers like this: