‘Yan Sanda A Abuja Sun Yi Awon Gaba Da Masu Zanga-Zangar Kawo Ƙarshen SARS

  • Home
  • Labarai
  • ‘Yan Sanda A Abuja Sun Yi Awon Gaba Da Masu Zanga-Zangar Kawo Ƙarshen SARS

Wasu mutane a Najeriya na cigaba da zanga-zanga kan rashin imani sa suke ce ‘yan sanda na yi a ƙasar. Ana zargin sashen ‘yan sanda na musamman dake yaƙi da fashi da makami (SARS) da cin zarafi tare da yin amfani da ƙarfin da ya wuce kima.
A yau a Abuja, mutane sun fito don cigaba da wannan zanga-zanga, sai dai sun ci karo da jami’an ‘yan sanda da suka tarwatsa su ta amfani da barkon tsohuwa da kama wasu daga cikinsu, ana danna su a mota.

Wannan zanga-zanga ana cigaba da yin ta ne a faɗin ƙasar, a wani ganmani da ake na ganin an kawo ƙarshen abin da wannan sashe na ‘yan sanda ke yi ga matasa.

A kwana uku da suka gabata, ‘yan Najeriya na kira ga a rushe wannan sashe na ‘yan sandan. Ko a jiya a jihar Ikko, ‘yan zanga-zangar sun haɗu a bakin majalisar jiha, inda suka kwana a gurin.

Duk da cewa hukumomi a mataki daban-daban na ƙoƙarin takawa abin birki, ana cigaba da zanga-zangar a Ikko da Badun da wasu ɓangarori a ƙasar.

Tags:
%d bloggers like this: