Sojojin Sama Sun Yi Nasarar Yin Ruwan Wuta Ga ‘Yan Ta’adda A Jihar Kaduna

  • Home
  • Labarai
  • Sojojin Sama Sun Yi Nasarar Yin Ruwan Wuta Ga ‘Yan Ta’adda A Jihar Kaduna

Ana cigaba da samun nasara wajen kakkaɓe ‘yan ta’adda dake hanyoyi da iyakokin Kaduna.

Shadkwatar tsaro ta Najeriya ce ta sanar da haka. A sanarwar da suka bayar, ta nuna yadda rundunar ta yi amfani da ISR don gano bukkokin ‘yan bindigar a dajin Kuyambana, inda suka yi musu ruwan wuta.

Shadkwatar tsaron Najeriya ta ce rundunar sojin sama ta ‘Operation Thunder Strike’ ta yi ruwan wuta ga wata maboyar ‘yan bindiga, inda ta samu nasarar kashesu a daji da kuma jihohi masu iyakoki da jihar Kaduna.

Shugaban yaɗa labarai, Manjo Janar John Enenche ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis a Abuja, inda ya ce wannan sabon shiri ne na rundunar sama ta “Operation Kashe Mugu 2”.

%d bloggers like this: