DADASARE DA TURAWA DA I’ITIQADI DA RUBUTUN TARIHINTA DA TA YI MAI DAUKE DA TAKAICI

  • Home
  • Adabi
  • DADASARE DA TURAWA DA I’ITIQADI DA RUBUTUN TARIHINTA DA TA YI MAI DAUKE DA TAKAICI

Na gama karanta tarihin rayuwar Hajiya Mama Dadasare Abdullahi da ta rubuta, It Can Now Be Told, masoyiya ga Baturen mulkin mallakar nan da yake daya daga cikin wadanda suke a gaba-gaba wajen dabbaqa Adabin Hausa, wato Dk RM East.

Labarin yana da ban takaici. Bayan sace ta da aka yi tana ‘yar kimanin shekaru 11 a shekarar 1929 tun a fari, kuma aka riqa lalata da ita, duk da wannan qarancin shekaru, barawon nata, Baturen mulkin mallaka wanda kawai da ‘Maisikeli’ take iya kawo sunansa, sai ga shi ya koma Birtaniya tare da barin ta da dan shegen da ta haifa masa, wanda zazzabin cizon sauro ya hallaka.

Ita kuwa a lokacin sai ta kasa jure wa komawa rayuwarta ta baya, hakan ya sa da kanta ta bi wani Baturen da ta fuskanci nutsattse ne yana qaunarta kuma zai kula da ita in aka kwatanta da wancan. Shi dai wannan Baturen, daya daga cikin marubutan Hausa na Boko na farko-farko, har hana ta ya yi ta bar addininta ta koma Kirista, saboda ba ya so ta barranta da al’umarta da irin tsarin rayuwarsu.

A iya cewa, hatta Fulakun Dadasare sai da ya subuce, wato jinin Fullancinta ya salwanta saboda irin yadda ta zama tamkar Baturiya. Domin ta rasa imaninta saboda yadda ta kasance ba ta ga tsuntsu ba ta ga tarko a qarshen rayuwarta. Wato ba ta iya ta bar wa Allah al’amari ba yayin damuwa ko fidda rai, sai ta zabi kashe kanta (irin danyen hukuncin nan na Turawa).

Lokacin da take a raye, ta kasance wata kafar mu’amala tsakanin Turawa da mutanen Arewa. Takan wayar da kai tare da qoqarin tseratar da mutan Arewa daga jahilci, sannan ta dimanci koyar da tsabta. Ita ce ta fara kasancewa macen da ta fara rubutun Boko, ga ta ‘yar jarida, malamar makaranta, mai fafutukar tallafa cigaban mata. Ga ta kuma ma’aikaciyar lafiya da sauransu.

Ta taba komawa Kirista duk da masoyin nata Dk RM East bai so hakan ba. Daga baya ta dawo Musulmarta lokacin da ta lura da yadda masu wa’azin Kirista suke aibanta Fulanin Jahadin Shehu. Addinin Musuluncin da har ta mutu tana cikinsa. Za kuma a iya cewa, tana riqo da shi sosai) duk da cewa akwai rudanin kashe kanta din da ta yi abin da Musuluncin bai yarda da shi ba).

Na kasance mai son labaran ban takaici, ina ganin sai irinsu ne fitattu ma. Hakan ya yi tasirin da ni ma ire-irensa nake rubutawa a matsayin marubuci. Masu karatu sukan yi qorafi, suna ganin da niyya nake kawo wa taurarina sanadin munana daga qaddarar da ke afka wa rayuwarsu. “Me ya sa ba za ka bar su suke cimma nasara ba ne? Me ya sa ba za ka bar su su rayu ba duk da iftila’in da yake fada musu, ga dimbin tasgaro da sarqaqiya, duk da kyawun aqidunsu, duk da siffofinsu na taurari ne mutanen kirki?” A zahiri ma wasu sukan kalli abin wai ni ba gwanin ba da labari ba ne.

Kar kuma ka dauka ko tasirin uban Falsafa Bagirken nan, wato Aristotil ne ya sa nake son labaran ban takaici. Ko kusa, hasali ma na taso da son irin labaran ne kafin na san wani wai shi Aristotil.

Amma yau ga shi a labarin rayuwar Dadasare da ta rubuta da hannunta, wasu suka buga, na fahimci irin takaici da jefa tausayin da nake jarrabtar masu karatuna a labarta musu labaran kaico da nake qagowa.

Babban al’amari, kuma abin da ya fi tsaya min a rai shi ne, hanyar da ta bi ta bar duniya a matsayinta na Musulma. Wato wannan kashe kan nata da ta yi wanda ba a iya gano takamaiman dalili ba har yau, ko da masharhanta da manazartanta kamar Dk Aliya Adamu ta Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato, wato UDUS. Amma rai dai, wai an cire wa fara kai.

Daga bisani, na zargi sanadin tasiri da rudin Tunani irin na Turawa. Wato su ne suka juyar mata da tunani. Domin lallai na kadu har ji nake kamar wata ‘yar uwata ta jini ce abin ya faru a kanta. Na kwana da tambayar, shin me ya sa za ta kashe kanta?

Yadda abin ya faru kuwa, shi ne, bayan ta ce, daga washegari ba za a gan ta ba. Da safe kuwa sai zuwa ta yi kawai ta fada rijiyar tsakar gidanta a shekarar 1984.

Ni ina da tunanin aqidun Turawa ne suka bata mata tunaninta na ‘yar Afirika, Musulma, ‘yar Arewa, Bafullatana. Haqiqannin gaskiya, ba a san mu da irin wannan dabi’ar ba.

Dole na ji takaici, kuma qarshe wajibi ne na wasa alqalamina, na sake rubuta sababbin labarai da zan huce zuciyar makaranta labaraina. Zan rayo da wani mataccen taurarona jarumi, kuma na ba shi wata sabuwar rayuwar da zai rayu a labarin.

Saidai abin kaico ne. Labarin Dadasare bai kasance qagagge irin nawa ba, balle a rayo da ita ta, komai qarfin basira ko fasaha ko zalaqar marubuci ko iya amfani da zabin kalmomi ko alqalaminsa.

Malaman Adabi (musamman na Turanci da suka zurfafa ta kan falsafa) ba sa wani bambanta al’amarin gaske ko qagaggun labarai da na gaske ko kuma tarihi mai gambiza da ake cewa tarihihi, matuqar kuwa ana maganar nazari da sharhi a turbar Falsafa dib. Wai duka daya ne a ganinsu.

Daga Hasheem Abdallah

Tags:
%d bloggers like this: