TASIRIN MARUBUTA DA GUDUNMAWARSU A ƘARNI NA 21

  • Home
  • Adabi
  • TASIRIN MARUBUTA DA GUDUNMAWARSU A ƘARNI NA 21

Tun lokacin jahiliyya, marubuta na da mihimmanci a al’umma. Domin kowacce ƙabila na da marubutanta na musamman. A wannan lokaci, duk ƙabilar da ba ta da marubuta, yakan zama abin gori da koma baya a gare su.


Da rubutu ne, musamman waƙa suke isar da saƙonni. Koda an taɓa ƙabilarsu, kafin a ce abu ya kai ga ɗaukar makami, marubuta ne za su fara mayar da martani.


An yi wani fitatcen mawaƙi kafin zuwa musulunci a ƙasar Larabawa da ake kira Zuhayr Bin Abi Sulma, wanda ya fito daga Banu Muzaina. Wata waƙa da ya rubuta akan haɗa kai da daina ɗaukar fansa akan yaƙe-yaƙen Larabawa ta yi shaharar da ta ɗaga mutunci da martabar ƙabilarsu. Wannan waƙa sai da aka rubuta ta da ruwa gwal aka rataye ta a ɗakin Ka’aba. Wanda a baya ƙabilarsu ba ta kai matsayin da za a rataye rubutunsu a Ka’aba ba. Saboda ɗaga darajar ƙabilarsu, sai da ya zamo duk wata bazawara a wannan ƙabila an aureta.


Marubuta sun kasance mutane ne masu daraja a al’umma, saboda sune fitila dake haskawa al’umma yadda rayuwa ta sa gaba. Mutane ne masu hikima da fikira tare da hangen nesa. Akoyaushe suna ƙoƙarin nazartar al’umma, walau ta hanyar karace-karance ko ta nazari, kula, bibiya da tariyar baya.


A wannan zamani ma haka abin yake, domin samuwar marubuta ya taka rawa a tarihin cigaban duniya. Marubuta iri-iri sun bayar da gudunmawa, waɗanda suka ƙunshi marubutan wasan kwaikwayo, rubutun zube ko na waƙa. Kai har da marubuta a ɓangaren aikin jarida da marubutan da ba na rubutun ƙirƙira ba.


Irin waɗannan gudunmawa ta shafi ɓangarori da dama da suka shafi tattalin arziƙi, da siyasa, zamantakewa, addini da al’ada, tsaro, da ilimin sana’oi, ilimin kimiyya da fasaha da sauransu.


A wannan ƙarni na 21, abubuwa sun sauya a tarihin duniya. An shiga wani zamani da Turawa suka yi wa laƙabi da globalisation, wanda aka ɗauki duniya kamar wani ƙaramim ƙauye ne da kowanne ɓangare ya san me ɗan uwansa yake ciki, ko kuma abin da ya shafi mutum ɗaya ya shafi mutane da yawa.


A yau, a wannan duniya da muke ciki, matsalar tsaro ta shafi kowanne ɓangare. Domin idan wata ƙasa ta shiga rikici da yaƙe-yaƙe, kafin wani lokaci sai ka ji ɓullar su a wata ƙasa. Misali, ƙasar Libya ta shiga halin yaƙi da taɓarɓarewar tsaro, wanda kafin wani lokaci, rikici da yaƙe-yaƙe sun yaɗu a wasu sassa na Afirika dake maƙwabtaka da su.


A yau matsalar sace-sace, fashi da makami, da satar mutane, fyaɗe da shaye-shaye ya zama matsalar kowa. Abubuwan da a tarihi wasu yankuna ba su san da su ba, yanzu sun addabe su. Ko a wannan lokaci da cutar Korona ta ɓulla a ƙasar Chana, ta gama game duniya, saboda cigaban da aka samu ta kowacce fuska da kasancewar duniya abu ɗaya.


A cikin wannan tafiya da ake ta sabuwar duniya a ƙarni na 21, samun bayanai da ilimi ya zama kamar ƙiftawar ido, duba ga cigaban da aka samu a kafofin sadarwa na yanar gizo da fasahar zamani a ɓangaren na’ura mai kwakwalwa. Wannan cigaban ya game kowanne ɓangare na rayuwar al’umma.


A wannan lokaci, wacce irin gudunmawa marubuta za su bayar wajen cigaban al’umma? To, gudunmawar da za su bayar ba ta da banbanci da wadda magabata suka bayar a baya. Amma a wannan zamani dole salo da tsarin isar da saƙo ya banbanta. Dole marubuta su tafi da zamani idan suna son yin tasiri a wannan tafiya ta sabuwar duniya.


Da farko dai sai marubuta sun tafi da kafofin sadarwa na zamani da ake da su irin su Facebook, Twitter, Youtube, Instagram, linkedin, whatsapp da sauransu. A yau akwai ɗinbin manhajoji da ake hada-hada a cikinsu, wanda rubutu na kan gaba a wannan tafiya.


A cikin waɗannan kafofin sadarwa, akwai miliyoyin al’umma, wanda babu irin sharar da ba za ka samu ba. Don haka, wajibi ne marubuta su banbanta da ɗinbin mutanen dake cikin wannan kasuwa. To amma, ta ya ya za su banbanta kansu a cikin tarin mutanen dake cikin wannan tafiya?


A nan dole ne matsayinsu na masu ilimi da bincike, kuma fitilar al’umma ya yi tasiri a zuciyarsu. Wannan shi zai yi musu alƙibla, ya zamo duk wani abu da zai fito daga maɗallin kwamfutarsu ya zamo rubutu ne da ya sha banban da game gari.


Dole a samu bincike, nazari, kula, bin diddigi da bibiya a cikin rubutunsu. Wannan shi zai zama gishiri ko magin rubutu, wanda zai gamsar da mai karatu.


A nan ban yi amfani da kalmar gishiri da magi a yadda ake fassara kalmomin a rubutu ba. A’a, ina nufin dukkan abubuwa da zai gamsar da mai karatu, ya tsima shi tare da riƙe shi ko jan hankalinsa, da bashi ainahin hoton abin da marubuci ke son isarwa.

Idan kana rubutu akan rashawa da cin hanci, za ka yi nazari sosai tare da bin diddigi, yadda idan rubutun ya fito, ƙarya ne wanda aka yi akansa ya musanta. Wani marubuci Abdulaziz A. Abdulaziz, ya yi rubutu akan wata tsohuwar minista a Najeriya akan sahihancin takardun da suka sahale mata hidimar ƙasa. Wannan rubutu da ya amsa sunansa, sai da ya kai wannan minista ta yi murabus.

Wani taron ANA Kano na musamman

Haka ma wani marubucin ɗan ƙasar Ghana Anas Aremeyaw Anas da ya kware akan rubutun bincike da bin diddigi, ya bankwaɗo aikin rashawa da cin hanci a ɓangaren wasanni, wanda hakan ya yamutsa hazo sosai. Wannan bincike na shi ya sa wasu shugabanni da masu horarwa suka rasa kujerunsu.


Irin wannan salo yakamata marubuta su yi amfani da su wajen bada gudunmawa ga al’umma. Ana da buƙatar marubuta su yi rubutu akan abin da ya shafi mulki da gudanarwa, siyasa, shari’ah, tsaro, ilimi, kasuwanci da sauransu. Akwai abubuwa na daɗi da rashinsa sosai a wannan ɓangarori. Yin rubutu zai nusar da jama’a tare da kawo sabon tunani na cigaban da aka samu a duniya.


Wannan rubutu zai iya kasancewa na ƙirƙira, ko ba ƙirƙirarre ba. Idan ka yi rubutun ƙirƙira, dole ya kasance ka gabarta da jigonka akan dukkanin tsanikan rubutu, sannan a ƙarshe ka fitar da mafita ta hanyar da tsari da dokoki suka amince da su.


A ƙarni na 20, an ga irin gudunmawar marubuta irin su James Hadley Chase (Rane Lodge Brabazon) da Sidney Sheldon da Abubakar Imam da Chinua Achebe da Wole Soyinka suka bayar akan rayuwar da ake ciki a wannan lokacin. Marubutan ƙarni na 21, sai a ce muku ga fili ga mai Doki.

Daga
Zaharaddeen Ibrahim Kallah
zikallah@gmail.com
Twitter/Instagram @zikallah

%d bloggers like this: