Madugun Kwankwasiya Ya Buƙaci Gwamnatin Buhari Ta Janye Ƙarin Kuɗin Mai da Wutar Lantarki

  • Home
  • Labarai
  • Madugun Kwankwasiya Ya Buƙaci Gwamnatin Buhari Ta Janye Ƙarin Kuɗin Mai da Wutar Lantarki

Tsohon gwamnan Kano kuma madugun kwankwasiya, a babbar jam’iyar hamayya ta PDP, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, ya nemi gwamnatin tarayya ta janye ƙarin farashin kuɗin man fetur da wutar lantarki da ta yi, wanda ya ce za su ƙara jefa jama’a a cikin matsin rayuwa.

Madugun Kwankwasiyar ya bada shawara ga gwamnati akan ta toshe hanyoyin da kuɗaɗe ke zurarewa a maimakon ƙarin farashi.

Ya ce. “Ƙasashen duniya da yawa a yanzu, shugabanninsu na tausaya musu inda suke fito musu da tsare-tsare ta yadda za su samu sauƙin raɗaɗin wannan annoba ta korona, amma sai gashi a Najeriya a irin wannan yanayi aka shigo da duka na ƙarin farashin mai da wutar lantarki da dai sauran abubuwa.”

Tsohon gwamnan Kano ya yi wannan furuci ne a jihar Edo, inda ya kai ziyarar ƙarfafa guiwa ga magoya bayan jam’iyarsu PDP, gabanin zaɓen gwamna da za a shiga a jihar mako mai zuwa.

%d bloggers like this: