Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Janye Yajin Aikinsu

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya sun janye yajin aikin da suka soma a ranar Litinin, 7 ga watan Satumba.


Jaridar Daily Trust a yau ta ruwaito cewa shugaban ƙungiyar ta NARD Dakta Sokomba Aliyu ne ya tabbatar mata da janye yajin aikin ta wayar tarho. A cewarsa, za su fitar da matsayarsu da cikakken bayani akan yajin aikin.


A cikin tsawon wannan kwanaki na yajin aikin an ji gwamnatin tarayya na bada shawara da a yi amfani da likitoci masu bautar ƙasa don cike gurbin likitocin.


Gwamnatin ta bakin Ministan Lafiya,.Osagie Ehanire ya ce dole ne likitocin su ƙara haƙuri tun an yi ƙoƙarin biya musu mafi yawa daga cikin buƙatunsu.

Tags:
%d bloggers like this: