Fitatcen Mawaƙi Dauda Kahuta Rara Ya ce Ya Daina Yi Wa Buhari Waƙa…

  • Home
  • Labarai
  • Fitatcen Mawaƙi Dauda Kahuta Rara Ya ce Ya Daina Yi Wa Buhari Waƙa…

Fitatcen mawaƙin Hausa da aka sani da Dauda Kahuta Rara ya ce ya daina yi wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari waƙa har sai an biya kuɗi.

Amma a cewarsa, ba wasu makusantar Buharin yake so su biya kuɗin ba face mutanen gari, masoya Buhari.

Wannan furuci ya yi shi ne a hira da ya yi da tashar sashen Hausa na Radiyo Faransa.

Za a iya cewa musabbabin wannan hira ya samo asali ne, saboda muhawara mai zafi da ta karaɗe shafin sadarwa na zumunta inda jama’a suke neman shi mawaƙin don jin ko zai iya sake rera wata waƙa ga Buhari a wannan lokaci da ake cikin matsin rayuwa. Wasu na danganta nasarar shugaba Buhari da irin gudunmawar da mawaƙin ya bashi wajen yaƙin zaɓe.

Mawaƙi Rara ya ce shi har yanzu yana cikin jirgin Buhari, domin bai sauka daga layin da ya san shi ba.

%d bloggers like this: