Tsohon Ɗan Takarar Shugabancin Ƙasa, Atiku Abubakar Ya Ƙalubalanci Ƙarin Kudin Mai

  • Home
  • Labarai
  • Tsohon Ɗan Takarar Shugabancin Ƙasa, Atiku Abubakar Ya Ƙalubalanci Ƙarin Kudin Mai

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya a gwamnatin PDP, Atiku Abubakar ya nuna takaicinsa da ƙarin kuɗin mai da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi.


Ko a jiya an ji shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na kare wannan ƙarin kudin mai da wutar lantarki a taron shugabanin Afirika ta yamma da aka kammala ƙasar Nijar.


Tsohon ɗan takarar babbar jam’iyar adawa, wato PDP ya bayyana kansa a matsayin ɗan kasuwa da yake kallon abubuwa ta fuskar kasuwanci. Ya nuna cewa kamata ya yi idan farashin mai ya faɗi a duniya, kuɗinsa ma ya sauka.


Ya bada misali da kasashen Turai da farashinsa ya ƙara yin ƙasa fiye da yadda yake a 2019.
Ya bayyana haka a shafinsa na Tuwita inda ya ce.
“idan har da gaske gwamnati ta cire hannunta daga kasuwancin man, to ba kamata ya yi a ce ya yi sauƙi ba?” In ji Atiku.

%d bloggers like this: