Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Zai Kasance Shugaban Dindindin Na Majalisar Sarakunan Kano

  • Home
  • Labarai
  • Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Zai Kasance Shugaban Dindindin Na Majalisar Sarakunan Kano

A yau Talata Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi wa dokar da ta kafa sababbin Sarakunan Kano gyaran fuska. Sabuwar dokar ta amince da naɗa Sarkin Kano a matsayin shugaban dindindin na Majalisar Sarakunan jihar, kamar yadda gwamnatin jihar ta buƙata.

Kafin yin wannan gyara, dokar masarautu ta jihar ta ce za a riƙa yin karɓa-karɓa a shugabancin majalisar sarakunan jihar duk bayan shekara huɗu. Da wannan gyara, Alh Aminu Ado Bayero (Sarkin Kano) zai kasance shugaba na dindindin.


Wani ƙarin gyara kuma da aka samu a dokar, shi ne ƙarin adadin masu zaɓan sarakuna daga huɗu zuwa biyar.


Sai dai masani akan harkokin masarauta, Malam Ibrahim Ado Kurawa ya ƙalubalanci wannan ƙari da aka samu. A cewarsa ko lokacin da Turawan mulkin mallaka da suka shigo Kano, ba su yadda sun sauya tsarin masu naɗa Sarki ba. A ganinsa shigo da siyasa zai sa a wayi gari da samun sauyi, inda za a iya tsayar da wani Sarkin Kano koda bai fito daga gidan Dabo ba.

Shi dai wannan zama, an gudanar da shi a majalisa ƙarƙashin jagorancin shugabanta Abdulaziz Garba Gafasa.

%d bloggers like this: