Gwamnatin Najeriya Ta Karɓi Maganin Cutar Korona Na Rasha

  • Home
  • Labarai
  • Gwamnatin Najeriya Ta Karɓi Maganin Cutar Korona Na Rasha

A yau ne ma’aikatar lafiya ta Najeriya ta karɓi samfurin maganin Korona da aka haɗa shi, a ƙasar Rasha. Jakadan Rasha a Najeriya, Alexey Shebarshin ne ya gabatar da maganin ga ministan lafiya, Osagie Ehanire a wata ziyara da jakadan ya kai masa a yau Juma’a.


Shafin Twitter na Ma’aikatar lafiya ya wallafa hotunan ganawar tsakanin Ministan Lafiyar da kuma Jakadan na Rasha.
Za a iya tunawa, a watan da ya gabata ne ƙasar Rasha ta bayyana samar da maganin rigakafin cutar korona, wanda Shugaba Vladimir Putin ya tabbatar da ingancinsa.
Ana sa ran wannan magani zai kawo waraka da samun sauƙi na tashin hankali da duniya ta shiga akan wannan annoba ta korona.

%d bloggers like this: