MUHIMMANCIN ILMIN GA ‘YA’YA MATA

Ilmin mata, ilmin al’umma ne

‘Ya mace, wata makaranta ce wacce take ilimantar da al’umma, domin za ta haihu, ƙila cikin ‘ya’yan da Allah ya azurta ta da su, mata sunfi yawa.
Mu ɗauka ‘ya ‘yan bakwal ta haifa, biyar daga cikinsu mata, maza kuma biyu, to waɗannan matan, ko wacce a cikinsu al’umma ce; domin za tayi aure, kuma za ta haihu. Sannan waɗannan ‘ya’yan da ta haifa, ita ce za ta musu tarbiyya.


Ta ya ya za tayi musu tabiyya? Sai tana da ilimi. In ba ta da shi, ita kanta abar a yiwa ce.
Uwa ita ce mutum ta farko da ‘ya’yanta suke koya daga gareta, kafin suje makaranta a koya musu abubuwa da yawa, wanda da sun je makaranta malamai za su gane lallai waɗannan ‘ya’yan sun samu kulawa daga gidajensu.


Rashin ilimi ga ‘ya mace, yana jawo abubuwa da dama, wanda hakan sai yasa tayi ta yin ibada ba tare da sanin abin da take aikatawa ba daidai ba ne, kuskure ne, musamman abin da ya shafi tsarki da ita kanta ibadar.


Mu ɗauki jinin al’ada kasancewar ko wacce mace in dai takai munzalin balagarta tana yi. Allah ya ce, “Ku sanni, kafin ku bauta mini.” To ta ya ya zaki san Allah, har ki bauta masa, in har baki da ilimi? Ashe ilimin ‘ya mace yana da mutuƙar muhimmanci ga kanta, da kuma ‘ya’yanta da sauran al’umma baki ɗaya.


Ilimin zai taimaka mata wajen gyara lahirarta, da cin ribar zaman duniyarta, da tarbiyyantar da ‘ya’yanta, wanda ta hanyarta za a samar da al’umma ta gari, a dalilin ilimin da ita take da shi.


Ilimin ‘ya mace yana da muhimmanci ta yadda yakan ba ta kariya a gurin ɓata garin mutane. Alal misali, mu ɗauki talla wanda ya zama ruwan dare a yankinmu na Arewa ga ‘ya’ya mata, za mu ga yadda abubuwa da dama ke faruwa ga irin waɗannan matan da iyayensu ke ɗora musu talla. Abin mamaki, dukka-dukka abin da za a ɗaurawa yarinya bai taka kara ya karya ba, amma a haka za tayi tafiyayyiya daga nesa zuwa tashoshin mota, tana ta tamɓele akan hanya, wanda hakan yake baiwa wasu mazan damar tunkararta da ko wacce irin magana kuma cikin ko wani irin yanayi.


Babu yadda za ayi da iliminki, ki yadda ki sai da mutuncinki koda miliyan ɗari za a baki. Jikin da baki da abin da ya fishi, amma ki wofantar da shi ga mazan banza. Mu lura da kyau, ilimi nasa mace shigarta kaɗai ta zamar mata kariya daga mazan banza, ta yadda ko tun kararta ba za su iya ba, ballantana fuskar yi mata zancen banza. Amma fa ga ‘ya mace mai yin aiki da iliminta, kuma wacce ta san ciwon kanta ba ta bayyanawa mutane tsiraicinta.
Domin ko cikin masu ilimin, akwai masu take sani, wanda iliminsu baya amfanarsu da komai.
Don haka nake ƙira ga ɗaukacin al’ummarmu (musamman yankin Arewa), da mu bada muhimmanci wajen ilmantar da ‘ya’yanmu mata. Allah ya zaunar da mu lafiya.

Muhammad Bala Garba
22 August, 2020.

%d bloggers like this: