Mahaukata Ma ‘Ya’Ya Ne

Cikin ƙasa da wata ɗaya abubuwa na ta faruwa a yankinmu. Tun da aka ceci wani yaro da iyayensa suka ɗaure shi tsawon shekara bakwai, ake ta samun makamanta ire-iren rashin adalci da cin zarafi tare da danne hakkin ɗan adam, na kulle su ba bisa ƙa’ida ba.

Wasu daga cikin iyayen na tutiyar cewa shaye-shaye ko wasu laifuka na ‘ya’yansu ne yake sakawa suna kulle su. Akowanne tsarin mulki a duniya, ba daidai ba ne ka kulle ɗan adam na tsawon wannan lokaci, sannan babu abinci da kulawa.

Waɗanda ke gidan yari a ɗaure bisa zargin muggan laifiya da suka haɗa da kisan kai, fashi da makami da fyaɗe na samun kulawa da abinci mai kyau. Idan ba su da lafiya, akan ɗauke zuwa asibiti don kulawa daafiyarsu. A zahiri ba mu taba ganin wanda ya yamushe ya lalace, kamar yadda yaron da aka fara kubbutarwa ya zama ba.

A jiya kuma nake karantawa an ƙara samun wani mai shekara 55 a garin Rogo da aka ɗaure shi tsawon shekara 30. ‘Yansanda bisa jagoranci wani ma’aikacin karen haƙƙin ɗan adam ne suka ceto shi. Wai a cewar danginsa yana fama da lalular kwakwalwa, shi yasa aka ci zarafinsa da take masa haƙƙi na ɗan adam.

Shin wane irin ƙoƙari ‘yan uwansa suka yi na ganin wacce irin lalurar kwakwalwa yake fama da ita? Ko sun yi ƙoƙarin kai shi asibiti? A hoton da aka nuno, an kafe shi a wani gungumemen icce, wanda sai da aka sa zarto aka yanke.

Wannan bawan Allah da tun yana shekaru 25 yake ɗaure, ya ya yake uzurin rayuwa, musamman fitsari da bayan gari? Ina mamakin yadda ya iya jure zama ba tare da matsalar zagwanyewar mazaunai ba. Ko suna sarara masa ya huta? Ko ya ya abin yake, ba a kyauta ba.

A lokacin da ‘yan takarar neman kujerar shugabancin Jami’ar Bayero ke zagayen campaign, Dr Sani Lawan Malumfashi ya ƙalubalanci wani daga cikin ‘yan takarar me zai yi dangane da gazawar jami’a na warware wasu matsaloli da suka shafi al’umma.

A sashen da yake, ya bada misali da cewa mutane da dama a al’umma na fama da ciwon damuwa (depression), amma ba a fahimta. Ya bayyana yadda Jami’a za ta taka rawa wajen ire-iren waɗannan matsaloli.Haƙika na yarda da shi wasu cututtukan kwakwalwa na faruwa ne saboda wasu dalilai da za a iya magance su.

Abin da nake so cewa anan shi ne, mutane na da gazawa wajen bibiyar ainahin matsala. Sannan ba sa jin wani nauyi yayin ɗaukar wani hukunci da babu hankali.

A ƙauyukanmu wasu matsaloli kan sa mutum ya shiga wata lalura, musamman saboda wasu rigingimu irin na su. Walau ko kan rabon gado da ko neman aure ko gona da sauransu, wanda ke kaiwa a yi abubuwa marasa daɗi.

Da inda aka san abin da yakamata ne, sai su ɗauke shi a kai asibitin masu rangwamen hankali. Rashin ɗaukar wannan hukunci zai sa a yi zargin ko akwai wata a ƙasa da suke ƙoƙarin rufewa.

Shekaru da dama, an yi wani gida da yake makwabtaka da gidanmu. Muna kiran gidan gidan kara, saboda da kara aka zagaye shi. Matar gidan ta samu lalurar kwakwalwa, wanda ta kai ‘yan uwan sun sa ta a wani ɗakin langa-langa suka kulle.

Ɗaki ne da babu taga, babu silin. A haka take zaune, da zafi da sanyi ko damuna. A wani lokaci aka wayi gari maigidan ya yi tafiya, sai babban ɗan maigidan wanda yake mitar uban na da gidaje masu kyau a cikin gari ya ƙi komawa ya zo ya tarwatsa gidan, inda ya yi tutiyar zai kunnawa gidan wuta.

Saboda rashin sanin hakkin ɗan adam da ko inkula na mutane, suka watse aka bar wannan mata ita kaɗai. Sai da matar nan ta kwana uku babu abinci babu ruwa, tun tana waƙenta a cikin ɗakin langa-langa, sai da ta koma kuka. Sai da iyayenmu suka ja hankalin abin da yake faruwa sannan aka zo aka ɗauke ta. Ashe idan da ba a yi magana ba, sai ta mutu a kulle. Ashe inda ya kunnawa gidan wuta haka za a barta.

Babu wata matsala da iyaye ko ‘yan uwa za su ɗauki doka a hannunsu ba tare da la’akari mai dokar ƙasa ta gabatar. Haƙiƙa hukuma na da rawa da zata taka a irin waɗanna abubuwa, domin damarta ne ta kare lafiya, dukiya da hankalin al’umarta.

Idan iyaye ko ‘ya’ya ba za su iya ɗaukar nauyin da Allah ya ɗora musu ba ta hanyar da ya dace, dole ne a dangane da hukuma. Na yabawa maƙwabta da suke kawo ɗauki na tona asirin ire-iren waɗannan matsaloli da bai kamata a dinga samun su b a ƙarni na 21.

Daga

Zaharaddeen Ibrahim Kallah

zikallah@gmail.com

%d bloggers like this: