Sojojin Kasar Mali Sun Kama Shugaban Ƙasar

A yau Talata sojojin ƙasar Mali suka kama shugaban ƙasar Ibrahim Boubacar Keita da Firaminista. Kama shi ya faru jim kaɗan bayan kungiyar ƙasashen Yammacin Afirka, (Ecowas) da ƙasar Faransa sun yi allawadai da harbe-harben da sojojin suka yi a sansaninsu da ke babban birnin ƙasar Bamako.


Tashar BBC Hausa a shafinta ta ruwaito cewa an kama shugaban ƙasar a gidansa da ke Sebenikoro, Bamako da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a agogon ƙasar. Shugaban yana tare da Firaiminista, Boubou Cissé, da ɗansa, da mataimakinsa Karim Keïta.


Wannan kamu ya biyo bayan matsin lamba da shugaba Ibrahim Boubacar Keïta yake fuskantar na ya sauka daga mulki inda ake yin zanga-zangar adawa da shi.


Mutanen ƙasar na nuna fushi daga halin da tsaro ke ciki a ƙasar inda rikice-rikicen ‘yan ta’adda da na ƙabilanci ke ta ƙaruwa.Sannan akwai ƙaruwar cin hanci da tabarbarewar tattalin arziki.


Dama a yau Talata ƙungiyoyin hamayya a ƙasar suka sha alwashin ci gaba da gagarumar zsnga-zanga, inda za a yi babban maci a ranakun Juma’a da Asabar.


A ɗazu tsohon shugaban ƙasar Najeriya Goodluck Jonathan, wanda ke jagoranta kawo sulhu a ƙarƙashin ECOWAS ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari don sanar da shi halin da ake ciki. Wannan zama na sirri da suka yi wataƙila na da alaƙa ga bayanan sirri da aka samu na abin da ka iya faruwa.

Tags:
%d bloggers like this: