OSHIOMHOLE YA MAGANTU KAN DAWOWARSA KUJERAR SHUGABANCIN APC

  • Home
  • Labarai
  • OSHIOMHOLE YA MAGANTU KAN DAWOWARSA KUJERAR SHUGABANCIN APC

Tsohon shugaban jam’iyar APC, Adam Oshiomhole ya magantu kan zargin da ake yaɗawa cewa yana ƙoƙarin dawowa kan kujerarsa ta shugabancin jam’iyya.


Ana iya tunawa, an sauke shi ne saboda rikicinsa da magajinsa, gwamnan Edo, Godwin Obaseki. Yayin da yake magana da ‘yan jarida a fadar gwamnati, bayan ganawarsa da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a jjya Litinin, Oshiomhole ya bayyana cewa babu wannan magana.


A kwanakin baya, POLITICS NIGERIA ta ruwaito cewa Babban Daraktan Progressives Congrss Forum (PCF), Salihu Lukman ya yi iƙirarin cewa Oshiomhole na tsara yadda zai dawo a matsayinsa na shugaban jam’iyya.


Da yake maida martani akan wannan zargi na Lukman ya ce;


“Kuna so na shiga faɗa ne da Alade? Shi Alade a ɗabi’arsa ƙazami ne, to ya ya zaka sa fararen kaya sannan ka tunkare shi. Kana ganin a cikin kaftanina zan je na yi faɗa da Alade? Ba zan yi ba.


“Kuna ji, ina son ‘yan jarida su yi bincike. Lokacin da aka sauke ni daga shugabancin jam’iyya na ƙasa, Edo a ƙarƙashin APC take… Shin sai na ci Edo sannan zan zama shugaba? Na yi kama da mara aiki? Shekarata 68. Abin da ba su fahimta ba shi ne, ba ofishin shugaban jam’iyya ba ne ya mayar da ni abin da nake ba a yanzu.


“Mara kwakwalwa ne zai ce Oshiomhole na son komawa shugabancin jam’iyyar ƙasa. Saboda me? Ku je ku bincika.”


A ƙarshe ya bayyana cewa ya je gurin shugaban ƙasa ne don ya yaba masa bisa shugabancinsa, sannan ya ƙara jaddada biyayyarsa.

Tags:
%d bloggers like this: