Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya Ta Sako Ghali Na’abba

  • Home
  • Labarai
  • Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya Ta Sako Ghali Na’abba

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta sallami tsohon kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Ghali Umar Na’abba bisa sammacin da ta yi masa tun a ranar Juma’a.

Tsohon kakakin majalisar ya shafe sa’oi biyar a hannun hukumar yana amsa wasu tambayoyi.
Ghali Umar Na’abba ya soki shugaba Buhari ne a wata hira da ya yi ranar Alhamis a tashar Channel TV, inda ya yi ikrarin ƙungiyarsu ta National Consultative Front (NSF) za ta kawo sauyi a Najeriya, tare da ba mutanen ƙasa irin rayuwar da suke buƙata.


Kakakin ƙungiyar ta NCF Dr Tasiu Yunusa ya bayyanawa Sahara Reporters a ranar Asabar cewa shugabansu Ghali Umar Na’abba ya samu sammacin hukumar tsaro ta farin kaya, kuma zai amsa wannan gayyata a ranar Litinin.


Jawabin yace: “Ku sani cewa DSS a ranar Juma’a ta bayyaci shugaban NCF kuma tsohon kakaki a Najeriya, Ghali Umar Na’abba, sakamakon hirar da yayi a tashar Channels Television ranar Alhamis da manufar kungiyar NCFront na samar da Najeriya da kowa zai ji dadi.


“Amma shugabanmu, Ghali Umar Na’abba, ya yanke shawaran amsa gayyatan DSS, kuma zai je hedkwatan hukumar dake Abuja ranar Litinin misalin karfe 12 na rana.”


Tsohon kakakin a baya ya zargi shugaba Buhari da sanya ƙasar Najeriya a halin da take ciki, kuma ya ce shi ne shugaba mafi gazawa a tarihin Najeriya

%d bloggers like this: