Mutane 1,689 sun warke daga Corona a rana ɗaya

  • Home
  • Labarai
  • Mutane 1,689 sun warke daga Corona a rana ɗaya

Sabuwar ƙididdigar hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta NCDC a Najeriya ta fitar da wasu alƙaluma a ranar juma’a dake nuna mutum 1,689 sun warke daga cutar covid-19 a rana ɗaya.


Sai dai a ranar ta juma’a an ƙara samun mutane 329 a faɗin ƙasar da suka kamu da cutar, sannan mutum 7 suka mutu.

Jumullar waɗanda suka kamu da cutar a Najeriya ya kai mutane 48,445, inda aka sallami mutane 35,998. Sai jumullar mutane 973 da suka mutu sakamakon cutar.

Tags:
%d bloggers like this: