Barcelona Ta Kwashi Kashinta A Hannu


A wasan da aka take jiya juma’a na gasar zakarun Turai, ƙungiyar kwallon ƙafa ta Barcelona dake Spaniya ta kwashi kashinta a hannu, bayan Bayern Munich ta Jamus ta kwararata mata kwallaye har 8 a raga.


Wannan shi ne karo na farko da aka taba yi wa Barcelona irin wannan cin mutunci, na ci 8 da 2.
Duk da cewa ‘yan wasa Barcelona irin su Messi da Suarex sun taka leda da ƙoƙarin sun kankare kwallayen, haƙansu ya kasa cimma ruwa.


Bayern Munich ta jefa kwallaye huɗu a raga kafin hutun rabin lokaci, wanda bayan an dawo zagaye na biyu suka ƙara zuba huɗu.


Yanzu dai Bayern na jiran wasan Manchester City da Lyon ta Faransa da za buga cikin daren ranar Asabar, domin sanin ƙungiyar da za su haɗu da ita a wasan dab da na ƙarshe.

Tags:
%d bloggers like this: