FARFESA SAGIR NA DAB DA ZAMA SHUGABAN JAMI’AR BAYERO

  • Home
  • Labarai
  • FARFESA SAGIR NA DAB DA ZAMA SHUGABAN JAMI’AR BAYERO

A kokarin da Jamiar Bayero ta Kano take na samar da wanda zai gaji shugabanci jami’ar, bayan karewar wa’adin shugabanci Farfesa Muhammad Yahuza Bello a ranar 17 ga watan Augusta, 2020, jami’ar ta Bayero ta yi babban taro na ma’aikatanta don zabar wanda zai gaje shi.


A yau Laraba aka gudanar taron, wanda ya kunshi tattaunawa da ‘yan takarar kujerar shugabancin jami’ar, tare da zaben wanda mambobin babban taron suke ganin ya dace ya jagoranci jami’ar. Al’ada ce dadadda a jami’ar, duk masu sha’awar wannan kujera kan samu dabar tattaunawa da mambobin wannan babban taro, inda ake musu tambayoyi kan manufofinsu, da cigaban da za su kawo wa jami’ar. Daga bisani sai a shiga zabe.


Bayan gudanar da wannan zama tare da jin manufofin kowa, an kada kuri’u masu yawa da suka bawa Farfesa Sagir Adamu Abbas damar lashe mafi rinjaye na kuri’un da aka kada. Domin ya samu kuri’u 1026, inda ya doke mai bi masa baya, Farfesa Adamu Idris Tanko da ya samu kuri’u 416.


Farfesa Sagir Adamu Abbas ya rike mukamai da dama a jami’ar ta Bayero, da suka hada da mataimakin shugaban jami’ar (DVC Academics) har sau biyu, sannan Darakta na Development Office da Darakta na cibiyar bincike da kirkira ta jami’ar Bayero. A wajen jami’ar, ya taba rike mukamin mataimaki na musamman ga tsohuwar ministar Ilimi, Farfesa Rukayyatu Ahmed Rufa’i (2010-2013), tare da mukamai da dama a ciki da wajen jami’ar.


Wannan dama da ya samu ta nuna yana gab da zama sabon shugaban jami’ar Bayero, domin yanzu ya rage kwamitin tantancewa su turawa Governing Council na jami’ar sunayen mutum uku da rahotonsu, wanda su kuma za su za sanar da wanda zai zama sabon shugaban jami’ar.


Ya zama al’ada a jami’ar ta Bayero, duk wanda ya yi nasara a zaben babban taro na jami’ar, shi yake kasancewa shugaban jami’ar, domin hakan na da alaka da cewa mafi yawan ma’aikatan jami’ar na son sa.


Sauran ‘yan takara guda biyu da suka shiga neman wannan kujera sune: Farfesa Muhammed Dikko Aliyu, daga jami’ar King Faisal dake Saudiyya wanda ya samu kuri’u 10, sai kuma Farfesa Dalhatu Balarabe Yahaya da ya samu kuri’u 5.


Kowane ne ya zama shugaban jami’ar, zai fuskanci kabulalen tafiyar da jami’ar na tsawon shekara biyar, wanda a halin yanzu jami’ar na kan ganiyar bunkasa dake bukatar kwararre don kaita kololuwar bunkasa, da kokarin ba ta yo kasa daga matakin da take ciki ba.
Daga
Zadeen Kano
dinik2003@yahoo.co.uk

Tags:
%d bloggers like this: