AN TAFI DA AISHWARYA RAI ASIBITI SAKAMAKON JINYAR CORONA VIRUS

  • Home
  • Labarai
  • AN TAFI DA AISHWARYA RAI ASIBITI SAKAMAKON JINYAR CORONA VIRUS

An tafi da Tauraruwar Bollywood Aishwarya Rai da ‘yarta mai shekaru 8 , zuwa asibiti a Mumbai don cigaba da jinyar Covid-19, da aka bayyana sun kamu da ita.


Mijinta Abhishek Bachchan tare da mahaifinsa, fitaccen tauraro nan Amitabha Bachchan na asibitin tun tuni, bayan kamuwarsu da Covid-19.


Amitabh Bachchan mai shekaru 77 da dansa Abshishek mai shekaru 44, na bangaren da ake killace masu wannan lalura. A lokacin da aka killace su, an bayyana lalular ta su ba ta tsananta ba.


Aishwarya Bachchan wacce take tsohuwar sarauniyar kyau ta duniya a shekara 1994, ta kasance daga cikin taurarin fim mafi daraja da suka kamu da wannan cuta ta coravirus.


A baya ta killace kanta, amma jaridar Times of India ta ruwaito cewa an tafi da ita asibitin Nanavati a ranar juma’a, bayan kokawa da ta yi na wahalar numfashi.

%d bloggers like this: