Ibrahim Magu Ya Yi Magana Don Kare Kansa

A bisa zarge-zargen da ake yi wa tsohon shugaban hukumar yaki da almundahana, rashawa da cin hanci (EFCC), Ibrahim Magu, ya fito ya yi magana bayan da aka sake shi daga tsare shi da aka yi na wasu kwanaki.


Ana zarginsa da laifuffuka da dama, wanda har jaridun kasar nan sun ruwaito cewa Magun ya bada wasu biliyoyin kudi ga mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo da fitatcen lauyan nan Femi Falana, SAN wanda duk sun fito sun karyata hakan.
Shi ma Magu ta bakin lauyansa, Wahab Shittu ya karyata hakan tare da wasu labarai da ake kitsawa na cewa an samu wasu kudade na gida da waje a gidansa.


Kusan sa’a 24 bayan samun ‘yanci, Ibrahim Magu ya rubuta takarda ga kwamitin shugaban kasa da ke binciken zargin badakala a EFCC, inda ya yi kokarin kare kansa.


Gidan talabijin na Channels TV, shi ya bada rahoton cewa Ibrahim Magu ya rubuta takardar ga shugaban kwamitin binciken, Ayo Salami.


Lauyansa Shiitu ya bayyana cewa wadannan duk labaran kanzon kurege ne da ake yadawa domin a bata sunan Ibrahim Magu da mataimakin shugaban kasa da kuma Femi Falana. Hakazalika ya musanta zargin cewa Magun yana da alaka da wani dan kasuwar canji a garin Kaduna.


Bugu da kari, Wahab Shittu ya bayyana cewa motocin da aka kwashe daga gidansa, wadanda hukumar ta ba Magu ne a matsayinsa na mukaddashin shugaba.


A karshe lauyan ya koka da cewa ba su samu takardar zargin da ake tuhumar wanda yake karewa ba. Ya ce da zarar sun samu takardar, Ibrahim Magu zai wanke kansa.

%d bloggers like this: