DA GANGAN AKA KASHE KAMFANIN JIRGIN SAMAN NAJERIYA

  • Home
  • Labarai
  • DA GANGAN AKA KASHE KAMFANIN JIRGIN SAMAN NAJERIYA

Harkar sufurin jirgin sama tana da matukar mihimmanci wajen cigaban kasa, domin tana sada mutane da kaya da kasashen duniya cikin sauri. A yau idan aka duba kasashen da suka cigaba, za a ga sun yi nisa sosai a harkar sufurin jirgin sama.


Kamfarin sufurin jirgi na Najeriya, Nigeria Airways ya kafu ne a 23 ga watan Agusta, 1958, a lokacin karkashin sunan West African Airways Corporation, Nigeria; wato (kamfanin jirgin sama na Afirka ta yamma). Daga bisani ya koma Nigeria Airways Limited. A wannan lokaci kamfanin ya taso da farin jini tare da gudanar da zirga-zirga a gida da kasashen ketare.


Kamfanin ya mallaki jirage har guda ashirin da uku lafiyayyu. A shekaru ashirin da biyar na farkon kafuwar kamfanin, ya bunkasa da shahara sosai, tare da fito da sunan Najeriya a fadin duniya. A wannan lokaci kasashe da suke da jirage na kasa irinsu Saudiyya da Ethiopia, duk a bayan Najeriya suke wajen yawan jirage da sanin harkar sufurin jiragen sama.


Kaico! Da tafiya ta yi tafiya, sai abubuwa suka sauya, har ya zamanto duk jiragen sun tarwatse sun lalace. Duk yawan jiragen da ake da su, guda daya ne kacal ya rage yana aiki. Wanda shi kansa ba ya samar da wata riba, domin ana amfani da cinikin da ya yi ne wajen shan mai kawai. In takaita, duk kokarin da aka yi na ganin kamfanin ya farfado sai da aka gaza. Hakan yasa aka rufe kamfanin gaba daya.


Abubuwa da dama sun faru da suka taimaka wajen durkusar da wannan kamfani. Ko shakka babu, ma’aikatan wannan kamfani sun taka rawa sosai wajen karyewar kamfanin. Domin kamar yadda ake daukar kayan gwamnati a wulakance a kasar nan, haka ne ya faru a kamfanin sufurin jirgin sama na kasa.


Ma’aikata sun yi gaban kansu, tare da yin wadaka yadda suke so. A cikin wannan lokaci na badakala, wasu ma’aikatan kan ba wa ‘yan uwa da abokai kyautar tikitin jirgin Najeriya su hau a kyauta, duk saboda alfarmar cewa na gwamnati ne. Sannan idan an tara kudade, sai a kashe su ba bisa ka’ida ba.


Ita kan gwamnati ta taimaka wajen karyewarsa, domin ita ke da alhakin sa ido da daukar matakai da suka dace. Baya ga wannan, akwai ma’aikatunta dake amfani da jiragen na kasa, wanda a ka’ida ana fidda musu kasafin kudade da za su yi zirga-zirgarsu a jirgin na kasa. Amma sai ya kasance ba a tura wannan kudade ga kamfanin sufurin na tafiye-tafiyen da aka gudanar. Kwata-kwata an sauka daga tsarin cigaba da dorewa na kasuwancin zamani. Wanda idan kamfani ne mai zaman kansa ne ba zai dauki haka ba.


Rashin jirgin dake dauke da tutar Najeriya ta haifar da matsala sosai ga ‘yan kasa, musamman ta bangaren zirga-zirga zuwa kasashen duniya. A yanzu duk wani da zai hau wasu jirage na kasashen duniya, dole sai ya tanadi manyan kudaden kasar waje na dalar Amurka, Sterling ko Euro. Ba inda za ka je a kasashen nasu su karbi naira, wanda hakan na kara matsi ga kasar Najeriya wajen neman wadannan kudade.


A yau idan za a bada misali da kamfanin jirgi mallakar kasa, dole a yi maganar Ethiopian Airlines. A lokacin da kamfanin Nigerian Airways ke sharafinsa, injiniyoyin Ethopian Airlines a Ikko ta Najeriya suke daukar horo tare da namu injiniyoyin. Amma yanzu shaharar Ethiopian Airlines ta wuce yadda ake tsammani.


Ya zama wajibi gwamnatin Najeriya ta fahimci kamfanoni masu zaman kansu ba za su iya taka wannan rawa ba, ta kiyaye ‘yanci da walwalar ‘yan kasa.


A lokacin da shugaba Buhari ya hau kan mulkin siyasa a karo na farko, ya dauki gabarar farfado da harkar jiragen sama na kasa karkashin Ministansa na harkar jiragen sama, Hadi Sirika. An kashe makudan kudade tare da neman kamfanonin da za a yi hadaka da su don ganin wannan harka ta tabbata. A wannan lokaci har an fitar da sabon logo, wanda zai bayyana sabuwar tafiyar da za a shiga. Amma sai aka wayi gari ministan harkokin zirga-zirga jiragen sama, Hadi Sirika ya fito ya bayyanawa duniya dakatar da wannan yunkuri, duk da irin kudade da aka kashe.


Wannan yasa ni cikin mamaki cewa shin a Najeriya, dama idan ana son gabatar da wani abu makamanci wannan, haka ake shiga babu wani tsari na ya ya za a tunkare shi, kuma mene ne riba da matsaloli da za a samu?


Hakan ya nuna ashe babu wani tsari da bature ke kira “Strategic Plan”. Domin sai da aka kashe makudan kudi, sannan aka fahimci wasu matsaloli da suka dakatar da wannan yunkuri. Da a ce an yi wannan bincike da tsari, za a iya fahimtar irin matsalolin da za a fuskanta da kuma hanyoyin da za a magance su. Sai dai kawai idan dama an shirya za a dauko wannan aiki ne saboda da wata manufa, sannan a yi watsi da shi bayan an cimma wannan manufa.


Lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta yi wa harkar sufurin jiragen sama garanbawul da yakamata don habaka tattalin arzikin kasa. Yakamata a samar da tsari (Strategic Plan) da zai haska na ya ya ake son harkar sufurin jiragen saman ta kasa ta kasance nan da shekaru masu zuwa. Domin an bar gini tun ran zane, an shigo da son rai da ya yi sanadiyar durkushewar harkar.


A da can ana da manyen filayen jirgi na kasa da kasa, wato filin jirgi na Malam Aminu Kano dake Kano da na Murtala Muhammed dake Ikko. Amma daga baya sai aka dinga karo su, ana ganin kamar birgewa ce. Samuwar manyan filayen jirage na kasa da kasa a fadin kasar ya taimaka wajen kashe kasuwar jiragen dake zirga-zirga a cikin gida.


Wasu kasashen duniya na da manyan filayen jirage na kasa da kasa masu yawa, amma kasashen da suke da hangen nesa ba sa tara manyan filayen jirage na kasa da kasa, saboda wasu dalilai. Misali, idan mutum zai yi tafiya irin wadannan kasashe, tun kafin ya tafi an bashi tikitinsa na jirgin cikin gida da zai hau idan ya sauka a babban filin jirgi na kasa da kasa. Wani lokacin ma ba lalle sai ya hau jirgin sama ba, zai iya kasancewa jirgin kasa zai bi. Wannan hikima ce da za ta samarwa masu jiragen gida fasinja tare da bunkasa tattalin arzikin kasa.


Yakamata mahukunta su duba wannan al’amari da idon basira, ta yadda za a ciyar da kasa gaba. A tawa fahimtar, kamar bangaren filin jirgin saman kasa da kasa na Abuja, zai iya zama kawai na saukar jirage kasa da kasa da suka shafi harkokin diflomasiya da karbar shugabannin kasashe ko wakilansu. Sannan zai fi kyau sauran manyan filaye na na kasa da kasa a rage yawansu zuwa biyu. Filin Jirgin Kano da na Ikko sun cancanci zamewa manyan filayen jirage na kasa da kasa da Najeriya za ta gudanar, yadda za a inganta su sosai daidai da makamantansu a duniya.


A wannan zamani na gasar tsira da kai, dole sai filayen jirage su zama na zamani cikakku da suka hada komai da ake bukata. Rashin kyawawan filaye zai iya kawo nakasu wajen cigaban harkar.
Idan an samu filaye masu kyau, sai ya zamo duk wanda zai zo Najeriya zai iya sauka a Ikko ko Kano, wanda daga nan sai ya hau karamin jirgi da zai sada shi da jihar da za shi.


Idan harkar sufurin jirage kasa na zamani ta inganta, za ta iya taimakawa, yadda fasinjoji za su yi amfani da ita. Ko ba komai kamfanonin jiragen saman gida da na jiragen kasa za su samu fasinja sosai, ta yadda zai bunkasa tantalin arzikinsu, wanda a karshe kasa ce za ta amfana.


Idan fasinja ya sauka a Ikko ko Kano, ko ba komai zai iya cin abinci kafin ya wuce inda za shi, hakan zai amfanawa tattalin arzikin kasar. Wadannan jihohi guda biyu, wato Kano da Ikko suna da dinbun al’umma da suka fi ko’ina yawa a fadin Najeriya. Sun kasance tsofaffun cibiyoyin kasuwanci da masana’antu. Wannan na kara nuna cancantarsu na kasancewa filayen jirage na kasa da kasa da za a yi amfani da su.


Najeriya ta kai matsayin da yakamata a ce akwai jirgi da yake yawo a duniya dauke da tutar kasarta. Harka ce mai riba wacce za a iya neman masu zuba jari su shigo ciki. Kasar na da abin da kowacce kasa take bukata wajen habaka harkar jiragen sama. Ko ba komai tana da arzikin yawan al’umma da suke harkokin kasuwanci a duniya, wanda na tabbata idan akwai jirgin sama na gida, wanda aka yi masa tsari mai kyau, babu wanda zai hau na waje ga na gida. Samuwar jirgin kasa na Najeriya zai iya tallafar kasashen na Afirka ta yamma, kamar yadda Najeriya ta somo a farko.


Hakika samar da jirgi na kasa dake dauke da tutar Najeriya na da matukar mihimmanci. Zai yi kyau idan ministan harkokin sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya yi waiwaye adon tafiya kan wannan yunkuri. Ko ba komai Allah ya ara masa lokacin a wannan kujera na tsawon lokaci, a waccan tafiyar da aka yi da kuma yanzu da ake damawa da shi. Wannan dama ce a gare shi ta ya rubuta sunansa da gwal, na sake bijirowa da tabbatar da wannan babban aiki. Allah ya taimaki Najeriya da shugabanninta.

Daga

Zaharaddeen Ibrahim Kallah

zikallah@gmail.com

@zikallah

Tags:
%d bloggers like this: