Matasa Ku Tashi Mu Gyara Najeriya

Hakika matasa ne kawai za su iya gyara Najeriya da taimakon Ubangiji. Najeriya kasa ce da Allah ya albarkace ta da dimbin jama’a, musamman matasa, wadanda ake yi wa lakabi da manyan gobe.


Sannan kuma matasa ne suka taka rawar gani wajen tabbatar da kafuwar kasar a baya. Duk wata kasar da ta ci gaba a duniya idan aka waiwaiyi sirrin da ke tattare da samuwar wannan ci gaban, za a ga a hannun matasansu ya ke. Saboda basu yin sakaci a fannin kulawa da rayuwar matasan ba.


Tun mu na kananan ake ce mana mu ne manyan gobe, mu ne magina kasa, amma gashi har yanzu mun kasa zama manyan, balle kuma mu gina kasar.
Yau a Najeriya an wayi gari, matasa ne da garkuwa da mutane, su ne da fashi da makami, shaye-shaye da zinace-zinace, luwadi da bangar siyasa, yawon bata gari da karya da cin amana da sauran aikin ash-sha.
Allah sarki kasar uwata Najeriya!


A baya dai matasa sun taka rawar gani sosai a sassa daban – daban na ci gaban Najeriya. Kusan za a iya cewa su ne kan gaba wajen tafiyar da al’amuran kasar bayan samun ‘yancin kanta.


Alal misali, shuwagabanni irin su Janar Murtala Muhammad da Janar Yakubu Gowon, sun shugabanci kasar su na matasa, duk da cewa dai shugabanci ne na soja, amma kuma sun taka muhimmiyar rawar gani matuka.


Sai dai kash! Matasa ayau sun zama kashin baya na ci gaban Najeriya, ba tare da la’akari da muhimmancinsu a cikin al’umma ba, da kuma rawar da zasu taka ta fannin gina kasa. Hakika wannan ya kamata ya zama kalubale ga mu kanmu matasa, don ganin martabarmu ta karbu a ko ina, ta hanyar kauracewa duk wani aikin ash-sha da dai sauransu.

Ganin cewa akwai bata gari a cikinmu, kuma Bahaushe ya ce wake daya shi ke bata gari. Saboda haka ya za ma wajibi a garemu da mu tashi tsaye, don ganin mun gyara kasarmu Najeriya. Mu kuma san cewa dabi’ar banza ba za ta haifar mana da da mai ido ba. Har ila yau, kada mu yarda mu zama ‘yan bangan siyasa, abin nufi a nan shi ne, kada wasu ‘yan tsirarun mutane su rinka amfani damu wajen tada zaune tsaye don kawai cimma burinsu, wanda bayan su wadannan mutane sun samu abin da suke so, basa yi mana komai illa su watsar damu.

Matasa ya kamata musan cewa mu wakilai ne na samar da zaman lafiya ba hargitsi ba. Komai na iya faruwa a duk lokacin da aka tauye mana hakkinmu ko aka ci gaba da nuna halin ko inkula dangane da rayuwarmu, musamman ma idan babu cikakken tsaro da ilimi da uwa-uba aikin yi da kuma sauran abubuwan more rayuwa wanda ya zama hakki ne na hukuma ta samar dasu. Rashin wadannan abubuwa zai iya jefa mu a tsaka mai wuya, kamar sace-sace da yawon banza da sauran aikin ash-sha da ba za a rasa ba, wanda kuma bama fatan ta sake kasancewa garemu.


Mu sa ni cewa, gyara Najeriya ba wai yana nufin aikin gwamnati ba, domin kowane matashi yana da baiwar da Allah ya basa, yayin da wani yafi wani, wani kuma dai-dai da wani, haka kuma basirar kowa tana iya bayyana ne idan mai ita ya maida hankali wajen koyon wani abu da yake sha’awa. Kana da nuna naciya wajen koyon wani abu da yaba da sha’awa, da lura da wasu abubuwa da wasu matasa keyi a rayuwar su. Wannan yasa wasu matasa masu kananan shekaru a kasar Amurka, suka shiga wata gasa inda su ka yi nasara da wasu abubuwa da suka kirkira kuma suka samu lambar yabo.


Ba komai ba ne yake sani takaici, illa yadda matasa mu ka yi sakaci da neman ilmi ayau. Ga mu da yawa tamkar kiyashi, amma miliyoyinmu sun kasa zuwa makaranta sai yawon banza. Ga mu da damamaki masu yawa, amma ba mu da aikin yi sai kallon kwallo da tadin kwallo da yawon banza. Ga mu da matasa da dama, amma mun ki yarda mu kirkirowa kanmu hanyar da za mu dogara da kanmu domin gyara kasarmu. Ga mu da malaman addini, amma basu da aikin yi sai tunzuramu mu yaki junanmu.


Haba matasa! Ina muka dosa ne a wannan kasar? Me muke nufi ne da wannan rayuwa? Ta ya ya za mu ci gaba da wannan gurgun tunani na mu? Shin irin haka kasashe irin su Amurka da Jamus da China suka bi har suka zama yadda suka zama a yau?


Gaskiya akwai matsaloli wadanda dole mu gyara su matukar dai muna so mu gyara Najeriya. Matukar muna son kasarmu ta ci gaba, to dole mu farka daga wannan dogon baccin da muke yi, mu yi aiki tukuru domin kasarmu ta gyaru. Matasa dole mu dawo cikin hayyacin mu, abu mafi muhimmanci da ya wajabta mu bayar da fifiko a kai, shi ne, neman ilimi. Domin babu wata kasa da ta ci gaba a duniya alhali tana yi wa ilimi rikon sakainar kashi. Dole mu dawo daga rakiyar mutanen da basa so su ga mun gano gaskiya. Dole mu dauki matakan amfanar da kanmu saboda a kauce ma kuskuren da wasu ‘yan uwanmu matasa suka yi a baya, kamar shiga kugiyoyin ta’addanci irinsu Boko Haram.


Ina kira ga ‘yan uwana matasa, mu zamo masu dogaro da kanmu, ta hanyar kirkirowa kanmu hanyoyin samun mafita na rayuwa. Hakan ne kadai zai fitar da mu daga takaicin rashin aiki da zaman kashe wando da muke fama da shi ayau. Ba wani dalilin da zai sa mu tsaya muna kiran ba aiki a kasa alhalin Allah ya yi mana baiwa da hikimar dogaro da kanmu, ta hanyar amfani da baiwar da Allah ya bamu na kirkirowa kanmu mafita, in har muna tsammanin ‘yan mazan jiya da suka dafe ko ina tun shekaranjiya har zuwa yau zasu daga mana kafa ne, to mu daina yaudarar kanmu, gara mu dawo kan tunanin kirkiro hanyar dogaro da kai.


Sau da dama mu matasa ba ma son motsa jiki kowa na jiran ganima daga gwamnati, wanda kuma wannan babban kuskure ne. Allah bai ce kowani dan Boko sai ya zama ma’aikacin gwamnati ba, kuma haka bai ce kowani ma’aikacin gwamnati sai ya zama mai kudi ba. Amma dai idan ka tsaya da kafarka ka jajirce, Allah zai baka mafita.


Ina jawo hankalin matasa ‘yan uwana, kar mu dauka da zaran mun kammala karatun Boko mun gama samun komai na rayuwar duniya. Lallai karatun Boko abu ne mai kyau, don zai haskaka mana hanyar da ya kamata mubi ta fuskar ilimi, amma ba abin dogaro ba ne wajen neman duniya da rufin asiri, don akwai da dama wadanda Allah ya yi musu arziki amma ko ajin furamare ba su taba shiga ba.


Zancen mutum ya zauna yana tunanin aikin gwamnati wannan ya kau, ya kamata mu zamu masu kwazo da himma wajen kirkirowa kanmu hanyar dogaro da kai, domin mafi yawan abin da ke cutar da mu ayau kenan, ragganci da sun ci a kwance don mun ga wani ya daukaka sai muce tilas sai mun zama kamar shi, wanda idan mutum ya yi rashin sa a, sai ya samu kanshi a mugun yanayi wanda kan jefa da yawanmu cikin danasani. Ya zama tilas mu zamu masu tunani, masu kwazo da hangen nesa, masu kokarin ci da guminmu koda kuwa aikin karfi mutum zai yi akwai dama sosai na yin hakan.


Da wannan nake kira ga gwamnati da sauran hukumomin da abun ya shafa, da su san cewa fa mu matasa ba abin wasa bane a kowace irin al’umma. Mutukar ana son Najeriya ta ci gaba dole a kula da rayuwar mu, musamman ma ganin cewa mu ne manyan gobe, domin muna da muhimmiyar rawar da zamu taka wajen ci gaban kasar. Don haka yana da kyau a rinka duba duk wata irin matsaloli dake damunmu, da kuma yin kokarin samar mana da maganinta. Ka na duk wata al’umma ko gwamnati da ta ga ayyukanta na samun cikas ko rashin ci gaba, to ta waiwaya ta dubi matasanta taga yadda al’amuransu yake tafiya.


A karshe ina kira ga dukkan matasan kasarmu, da mu tashi tsaye wajen neman ilimin addini dana zamani, sannan mu zamo masu dogaro da kai ta hanyar kirkirowa kanmu hanyoyin samun mafita na rayuwa. Idan muka tsaya akan haka, Allah zai dafa mana.
Ina rokon Ubangiji Allah ya yi mana jagora, yasa kasarmu da yankimu na Arewa su zauna lafiya, Amin.

Muhammad Bala Garba, Maiduguri.
2/2/2020.

%d bloggers like this: